Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Masu bincike na Masar sun ba da shawarar samfurin kwamfuta domin taimakawa ganowa da kuma magance COVID-19

Hausa translation of DOI: 10.1101/2020.04.16.20063990

Published onAug 14, 2023
Masu bincike na Masar sun ba da shawarar samfurin kwamfuta domin taimakawa ganowa da kuma magance COVID-19
·

Yanayin Ganowa da Tsinkaye don Karɓar Magani ga Majiyyacin COVID-19 dangane da Convolutional Neural Networks da kuma Whale Optimization Algorithm Ta Amfani da Hotunan CT

Ɓarkewar cututtukan coronavirus (COVID-19) ya bazu da sauri a duk faɗin duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya (HLD) ta sanar da cewa coronavirus COVID-19 annoba ce ta duniya.

Gwajin miyau da majina (RT-PCR) na cikin lokaci (RT-PCR) yana da ƙarancin inganci da amfani a farkon matakin COVID-19.

A sakamakon haka, ana amfani da Hoton Kwamfuta (CT) domin ganowa.

COVID-19 tana da muhimman alamomi daban-daban a kan sikan CT da ya bambanta da sauran ƙwayar cutar namoniya.

Waɗannan alamomin sun haɗa da wurare toka-toka da fararen wurare na hoton huhu da kuma shimfidar sassa mabambanta.

A cikin wannan takarda, an gabatar da Samfurin Aikin Na’ura don COVID-19 Ganowa da Tsinkaye domin Amsar Magani ga Majiyyaci (AIMDP).

Samfurin AIMDP yana da manyan ayyuka guda biyu da aka nuna a cikin ƙananan kayayyaki guda biyu, wato, Yanayin Ganowa (YG) da Yanayin Tsinkaye (YT).

An ba da shawarar Yanayin Ganowa (YG) domin ganowar wuri da kuma daidai gano majinyata masu COVID-19 da kuma bambanta shi da sauran cututtukan namoniya ta hanyar amfani da alamun COVID-19 da aka samu daga sikanin na CT.

Samfurin YG, yana amfani ne da Convolutional Neural Networks (CNNs) a zaman dabarar koyo Mai zurfi don rarrabuwa, yana iya aiwatar da ɗaruruwan hotunan CT a cikin daƙiƙoƙi domin hanzarta gano cutar ta COVID-19 da ba da gudummawa a cikinta.

Bugu da ƙari, wasu ƙasashe ba su da ikon ba duk marasa lafiya magani da ayyuka na kulawa mai zurfi, domin haka zai zama dole ne a ba da magani ga marasa lafiya da jikunsu zai karɓa kawai.

A cikin wannan mahallin, an ba da shawarar Yanayin Tsinkaye (YT) domin tsinkayar yin aikin magani ga majiyyaci bisa dalilai daban-daban misali, shekaru da matakin kamuwa da cuta da gazawar numfashi da gazawar gaɓoɓin jiki da yawa da kuma tsarin kulawa.

PM ya aiwatar da Whale Optimization Algorithm domin zaɓar siffofin majiyyaci mafi dacewa.

Sakamakon gwaji ya nuna kyakkyawan aiki domin samfuran ganowa da kuma tsinkaya da aka tsara, ta yin amfani da saitin bayanai tare da ɗaruruwan ainihin bayanai da kuma hotunan CT.


Masu bincike na Masar sun ba da shawarar samfurin kwamfuta domin taimakawa ganowa da kuma magance COVID-19

Masu binciken sun ƙirƙiri shirin kwamfuta na gwaji don ƙoƙarin gano farkon COVID-19 da sauri kuma tare da daidaito mafi girma.

Sun kuma samar da wani samfur domin hasashen yadda majiyyaci zai iya murmurewa da magani.

SARS-CoV-2, ƙwayar cutar numfashi da take haifar da COVID-19, ta bazu cikin sauri a cikin shekarar 2020 domin haifar da annobar COVID-19 ta duniya.

Gwajin miyau da majina (RT-PCR) shi ne gwajin da ya fi inganci wajen gano COVID-19.

Amma fa, yana iya zama kuskure a farkon matakan kamuwa da cutar. 

Da alama sikanin na na’urar ɗaukar hoto (CT) sun fi dacewa wajen gano cutar ta COVID-19 da wuri, amma akwai buƙatar ƙwararrun ‘yan’adam su tantance sikanin ɗin.

Tun da yawancin marasa lafiya masu COVID-19 suke mamaye asibitocin, ma’aikatan kiwon lafiya ba su da kayan aiki da za su yi maganin su duka.

Marubutan wannan binciken sun so su yi amfani da fasahar da ake kira “inji mai koyo” domin taimakawa ma’aikatan gaba-gaba wajen gano majinyatan COVID-19 daga sikanin na CT, ta yadda za su yi amfani da ƙarancin ma’aikata don kula da marasa lafiya da yiwuwar murmurewa.

Sun so su yi amfani da ainihin bayanan marasa lafiya masu COVID-19 domin koyar da shirin kwamfuta yadda ake gano COVID-19 daga sikanin na CT da kuma yin hasashen ko magani zai karɓi majiyyaci.

Sun kuma so su ƙara sauri da daidaiton yin gwajin COVID-19 ta amfani da sikanin na CT.

Waɗannan masu binciken sun sa wa shirin kwamfutarsu bayanan marasa lafiya (kamar sinanin na CT da sakamakon gwajin RT-PCR da kuma cikakken adadin jini) domin ta iya koyon gano cutar ta COVID-19 da ba da shawarar hanyar magani, duk bisa ga ƙwarewar ‘yan’adam ƙwararru na baya da suka gano da kuma kula da waɗannan marasa lafiya.

Masu binciken sun ce shirin nasu ya kai kashi 97% daidai kuma suna iya yin hasashen daga sikan na CT a cikin kusan daƙiƙoƙi 20.

Har ila yau, sun ce shirin nasu yana yin hasashen da ya fi dacewa a cikin gajeren lokaci fiye da yadda sauran masu bincike suka iya cim ma wa ta hanyar amfani da bayanai daban-daban.

Sauran ƙungiyoyin bincike sun duba bincikar COVID-19 ta amfani da sikanonin CT da kuma inji mai koyo.

Abin baƙin cikin shi ne, a cikin waɗannan binciken samfuran na’urorin ba su iya yin bayanin ganewarsu ta asali ba kamar yadda ƙwararren ɗan’adam zai yi; sau da yawa kawai suna bayar da cutar da kanta.

A cikin wannan binciken, masu bincike sun yi ƙoƙarin magance wannan matsala ta hanyar bayyana irin nau’in sikan na CT da kwamfutar take amfani da shi don gano cutar.

Masu binciken sun shirya gwada wannan samfurin a kan ƙarin bayanai domin tabbatar da sakamakonsu.

Sun kuma shirya yin sabon tsari wanda zai iya yin hasashen yadda marasa lafiya da suka kamu da COVID-19 suke.

Sun ce hakan zai taimaka wa likitoci su yanke shawarar yadda za a kula da mara lafiya yadda ya dace.

Tare da ƙarin bincike, wannan ra’ayin ƙungiyar bincike ta Masar na iya taimaka wa likitoci da yawa sarrafa iyakataccen albarkatu a yayin da suke kula da marasa lafiya da suka kamu da COVID-19.

Amma, dabararsu za ta buƙaci ingantaccen matakan samar da ababen more rayuwa, kamar injinan CT da kuma manyan kwamfutoci, waɗanda ƙila ba za su samu ba a yankuna da yawa na Afirka.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?