Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Shin haɗewar takin da gawayi za su iya haɓaka ingancin ƙasa mai tsananin yanayi a yankin sabana?

Hausa translation of DOI: 10.1016/j.heliyon.2021.e07089

Published onApr 04, 2023
Shin haɗewar takin da gawayi za su iya haɓaka ingancin ƙasa mai tsananin yanayi a yankin sabana?
·

Shin haɗewar takin da gawayi za su iya haɓaka ingancin ƙasa mai tsananin yanayi a yankin sabana?

Raguwar qarfin ƙasa babban cikas ne ga noman amfanin gona a yankin kudu da hamadar Sahara.

Marubuta da dama sun ba da rahoton ingantaccen tasirin gawayi da takin ƙasa akan amfanin ƙasa.

A wannan binciken, an yi gwajin xakin gwaji na kwanaki 30 ta hanyar amfani da samfuran 120 g na ko wanne na Haplic acrisol wanda aka gyara da gawayin ciyawar masara (cbio), gawayin vawon shinkafa (rbio), gawayin vawon kwakwa (coco300 da coco700) ko takin kaji (taki); da gawayin ruvavven vawon shinkafa (rcocomp) ko gawayin ciyawar masara (cococomp) a matakin gyara na 1% w/w: ƙasa, bi da bi.

Wasu gwajejen kan jinyar qasa a cikin binciken sun haɗa da takin kaji da gawayin masara ko vawon shinkafa (1% taki + 1% gawayi: 1% ƙasa w/w), bi da bi, don binciko tasirinsu a kan numfashin ƙasa, pH na ƙasa; qwayar halittar ƙasa; iyawa musaya; jimlar qwayoyin kabon, jimlar sinadarin niturogin da abubuwan da ake samu na niturogin.

Gawayi da takin da aka yi amfani da su kawai ko tare, da gawayin takin ya ƙara pH na ƙasa da 0.28-2.29 pH idan aka kwatanta da qasar da ba a gyara ba.

Numfashin qasa da ke fitowa daga takin da aka yi da takin shinkafa ko takin masara, ko haɗaɗɗen gawayi da takin sun fi ƙarfi kan wanda ba a gyara ba, wanda yayi kama da na gawayi kawai.

TOC a cikin takin da ba gauraya ba da wanda aka haɗa da gawayin masara, wanda aka yi wa jiyya sun fi wand ba a yi wa jinya ba da 37% da 117%, bi da bi.

Haɗe-haɗen amfani da gawayin vawon shinkafa da taki ya ƙara MBC da 132% yayin da ƙarin takin da aka haɗa ya qara MBC da 247%, bi da bi, idan aka kwatanta da wanda ba sarrafa ba.

A ƙarshe, binciken ya nuna cewa takin da ba a sarrafa ba da wanda aka sarrafa da gawayi, ya qara inganta sigogi ƙasa kamar pH na ƙasa da MBC, da kuma inganta daidaiton C na ƙasa ta hanyar inganta TOC da raguwar C na ƙasa.


Gawayi da taki yana inganta qasa don tsirai

Wannan binciken ya binciki yadda za a iya amfani da gawayi, wani abu mai qarko, mai yawan sinadarin kabon da aka yi daga sinadarin bayomas, da aka jefar, don inganta yanayin ƙasa a yankin Saharar Afirka.

Binciken ya gano cewa gawayi yana qara ingancin ƙasa kamar yadda sauran hanyoyin da suka fi tsada kuma ba su da sauƙi.

Raguwar qarfin qasa na xaya daga cikin manyan matsalolin da ke fuskantar noman amfanin gona a yankin kudu da hamadar saharar Afirka.

Ingantacciyar ƙasa za ta haifar da ingantacciyar amfanin gona, wanda zai rage talauci a yankunan karkara da kuma rage lalacewar albarkatun ƙasa

Bincike ya nuna cewa ana iya amfani da gawayi, wani abu mai ƙarfi mai yawan sinadarin kabon, don haɓaka lafiyar ƙasa.

Gawayin da ake magana akai shine samfurin dumama kwayoyin halitta, ko sinadarn bayomas, a yanayin qaranci ko rashin iska.

An nuna cewar gawayi yana ƙara sararin ƙasa, ƙara yawan ruwa da iska, kuma yana kunna ƙananan ƙwayoyin halitta a cikin ƙasa.

Wannan binciken ya gwada tasirin gawayi da taki kan ingancin ƙasa ta amfani da alamomi kamar numfashin ƙasa, pH na ƙasa, kasancewar ƙananan ƙwayoyin halitta, adadin sinadarin kabon, da adadin sinadarin naturogin da ake samu.

Masu binciken sun samar da gawayi daga ciyawar masara, kwakwa da vawon shinkafa ta hanyar amfani da qonasu, wato pyrolysis, wanda ya haxa da xumama kwayoyin halitta a yanayin da ba iskar, a 450C a cikin tukunyar gargajiya.

Masu binciken sun samar da gawayin kwakwa ta hanyar qonasu a 300C da kuma a 700C.

Daga nan ne masu binciken suka samar da samfuran ƙasa da aka gauraye da kwayoyin halitta na tsawon kwanaki 30.

Ko wane samfurin ya ƙunshi ƙasa da aka shirya ta musamman mai suna Haplic acrisol, wanda aka haɗa da nau'ukan gawayi dabam-dabam da aka yi daga masara, vawon shinkafa ko na kwakwa, da takin kaji.

Sauran samfurori sun ƙunshi cakuxa ƙasa da takin kaji, tare da vawon shinkafa, da ƙwayar masara, bi da bi.

Ko wane samfurin ya ƙunshi takin 1%, 1% na ko wane gawayi, domin masu binciken su bincika tasirin ko wane cakuxa a kan ingancin ƙasa.

Masu binciken sun gano cewa ƙara gawayi da takin a cikin ƙasa, ko dai daban ko tare, yana ƙara ƙimar pH na ƙasa daga raka'a 0.28-2.29 pH, idan aka kwatanta da ƙasa mara gauraye.

Ƙaruwar pH yana nufin asid ya ragu cikin ƙasar.

Binciken ya gano cewa numfashin, ko kuma mafi qarancin sinadarin kabon da qasa ke fitarwa, yana karuwa ne idan aka haqa takin kaxai, ko kuma idan aka haxa takin da gawayin vawon shinkafa, ko na masara ko gawayin garwaye.

Samfurorin ƙasan sun nuna ƙaruwar jimlar snadarin kabon ɗin da ya kai 37% idan aka yi amfani da takin kaɗai, da ƙaruwar 117% idan aka gauraya gawayin masara da takin.

Adadin motsin ƙwayoyin halitta ya karu da 132% inda ƙasa ke da cakuxar taki da gawayin vawon shinkafa, idan aka kwatanta da karuwar 247% a cikin samfuran ƙasa waɗanda ke da taki kawai.

Sakamakon wannan bincike ya nuna cewa yana iya yiwuwa a rage asid xin ƙasa ta hanyar amfani da gawayi, wanda ke da arha kuma yake samuwa cikin sauƙi.

Wannan ya bambanta da tsarin da ake bi na sassauta kasa, wanda ke da tsada kuma da wuya ga kananan manoma a yankin kudu da hamadar Sahara.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?