Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Kwaikwaiyo a kan amfanin gonakin ƙasar Zimbabwe ya nuna ingantaccen ingancin ƙasa zai iya rage illolin sauyin yanayi

Hausa translation of DOI: 10.1007/978-3-319-92798-5_5

Published onJun 01, 2023
Kwaikwaiyo a kan amfanin gonakin ƙasar Zimbabwe ya nuna ingantaccen ingancin ƙasa zai iya rage illolin sauyin yanayi
·

Fahimtar Rawar Ƙasa da Gudanarwa Suke Takawa a kan Amfanin Gona ta Fuskar Rashin Tabbas na Yanayi a Ƙasar Zimbabwe: Binciken Tsanaki

Tsakure

 Duk da cewa sauyin yanayi yana iya shafar ɓangarori daban-daban a ƙasar Zimbabwe, haɗarin da yake tattare da noma ya fi yin fice kasancewar noma shi ne jigon tattalin arzikin ƙasar.

Bugu da ƙari, akwai ƙarancin bayanai a kan yadda za a taimaka wa tsarin noma na masu ƙaramin ƙarfi da kuma abubuwan rayuwa don magance waɗannan haɗurra.

Domin tantance illolin a wajen samar da amfanin gona na canje-canjen da ake sa rai a cikin yanayin hazo da hasashen haɓakar iskar gas (CO2) da kuma zafi, mun yi amfani da samfurorin amfanin gona na tushen tsari guda biyu – samfurin Tsarin Taimakawa na Yanke Shawara don Canja Wurin Kimiyyar-Noma (DSSAT) da samfurin Tsarin Kwaikwayon Samar da Amfanin Gona Samfurin (APSIM).

An daidaita samfurorin da kuma tantancea don kimanta illolin de tasirin abubuwan yanayi guda ɗaya da haɗaɗɗu a kan aikin masara da kuma gyaɗa a cikin nau'o’in ƙasa guda uku.

Samfurorin biyu gabaɗaya sun yarda da illolin da yanayin yanayi daban-daban ke haifarwa a kan masara da gyaɗa, duk da haka, yawan illolin sun bambanta.

Alal misali, raguwar amfanin hatsin masara ya fi fitowa fili a cikin tsarin APSIM yayin da tsarin DSSAT ya nuna ƙarin raguwar yawan karan masara.

Duk samfurorin biyu sun nuna fa'idojin amfanin ƙasa a ƙarƙashin mayar da hankali kan haɓakar CO2 ga gyaɗa suna nuna rashin illoli na yanayin zafi da yan a lokacin kimanta illolin abubuwan yanayi.

Duk da haka, yawan amfanin gona na duka gyaɗa da suka ƙaru sun fi bayyana a cikin samfurin DSSAT.

Abu mafi girma da aka gano shi ne ƙasa tana taka muhimmiyar rawa wajen tantance sakamakon hulɗar amfanin gona da yanayi: za su iya jurewa ko kuma ƙara illolin yanayi.Kwaikwaiyo a kan amfanin gonakin ƙasar Zimbabwe ya nuna ingantaccen ingancin ƙasa zai iya rage illolin sauyin yanayi

 Wannan binciken ya kwaikwayi illolin sauyin yanayi a kan samar da amfanin gona a ƙasar Zimbabwe kuma ya gano cewa sauyin yanayin zafi da ruwan sama da kuma iskar gas suna yin illa ga yawan amfanin gona.

Duk da haka, maiyar da hankali kan ingantacciyar ƙasa yana iya rage illolin sauyin yanayi don kare yawan amfanin gona.

 Sauyin yanayi yana iya yin tasiri mummuna a fannin noma ƙasar Zimbabwe, babban jigon tattalin arzikin ƙasar, amma akwai ƙarancin bayanai da za su taimaka wa ƙananan manoma su don kaucewa haɗarorin.

Sauyin yanayi yana da yuwuwar canza yanayin ruwan sama da adadin iskar gas da ake samu, a dalilin haka yana tasiri ga samar da amfanin gona.

Sai dai ba a yi nazari sosai kan ainihin illar waɗannan canje-canjen a ƙasar ta Zimbabwe ba.

Saboda haka, wannan binciken ya duba tasirin canje-canjen da ake sa ran za a iya samu na ruwan sama, da ƙaruwar iskar gas (CO2), da yanayi, wajen samar da amfanin gona ta hanyar amfani da samfurorinlissafi guda biyu.

 Masu binciken sun yi amfani da waɗannan samfurorin guda biyu wajen tantance illolin sauyin yanayi guda ɗaya da kuma haɗaɗɗu abubuwan wajen samar da amfanin gonakin gyaɗa da masara a yankin Nkayi na ƙasar Zimbabwe.

Masu binciken sun yi amfani da samfurorin don kwatanta lokuta daban-daban, da rawar da matakai daban-daban na ƙasa kamar hawan ruwa da hawan nitrogen suke takawa, baya ga matsakaici da mafi ƙarancin yanayin zafi da amfanin gona zai iya fuskanta a tsawon yini.

Manazartan sun yi amfani da tsarin ne wajen gudanar da bincike kan tasirin da sauyin yanayi yake haifarwa ga hatsin masara da gyaɗa da kuma ganyaye da kuma ganyen da ake bari a gona lokacin girbi (wanda aka fi sani da kara).

 Binciken ya gano cewa samfurorin biyu sun yi ittifaki a kan illar da yanayi daban-daban suke da shi a kan masara da gyaɗa, duk da haka, girman tasirin ya bambanta.

Samfurin APSIM ya nuna cewa amfanin hatsin masara yana raguwa tare da sauyin yanayi, yayin da tsarin DSSAT ya nuna cewa karan masara yana raguwa sosai a sanadiyyar sauyin yanayi.

Dukkan samfurorin sun nuna cewa samar da gyaɗa ya ƙaru a mafi girman matakan iskar gas (CO2), amma samfurin DSSAT ya nuna mafi kyawun samar da hatsin gyaɗa da kara a yanayin zafi mai yawa da kuma matakan CO2.

Manazartan sun gano cewa ƙasa na taka muhimmiyar rawa wajen tantance yadda amfanin gona zai dace da canje-canjen damina da kuma zafi.

 Waɗannan sakamakon sun nuna cewa ingancciyar ƙasa mai kyau ita ce mabuɗin daƙile illolin sauyin yanayi a wajen samar da amfanin gona.

Masu binciken sun ba da shawarar cewa manoma da gwamnatoci a Afirka su mayar da hankali wajen inganta ƙasarsu don kare kansu daga tasirin sauyin yanayi.


Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?