Description
Lay summary for the article published under the DOI: 10.3390/antibiotics10040454
This is Hausa translation of DOI: https://www.mdpi.com/2079-6382/10/4/454#
Duk cututtuka na iya warkewa in har qwayoyi masu haddasa cutar na kamuwa da magani.
Yanda qarfin magungunan bakteriya ke raguwa ya zama hatsari mai matuqar tada hankali ga kiwon lafiya a faxin duniya wanda ke kawo barazanar janye magungunan bakteriya masu muhimmanci ga tsaida cutuka.
Qaruwar buqatar abinci da ake samu daga dabbobi, musamman qwai, nama da madara ya kawo yawan fito da su ta hanyoyi daban-daban, har da amfani da magungunan bakteriya ba bisa qa’ida ba.
Magungunan bakteriyan da manoma da masu lura da dabbobi marasa ilimin zamani ke amfani ko kula da su, na iya shiga yanayin da bai dace ba kamar rashin mizani, amfani a yanayin da bai dace ba, hanyoyin amfani da kuma lokutan daina amfani waxanda ba su dace ba.
An yi wannan binciken ne don fahimtar amfanin dokoki da shugabanci a magungunan bakteriya, a kuma fahimci hanyoyi da kuma yawan amfani da su, da kuma tantance burbuxin magungunan bakteriya da kuma rashin jin maganinsu cikin dabbobi da ake ci da kuma tsirrai da ake noma don gwada abinda da aka gano tare da hanyoyin da aka riga aka sani wajen magance rashin jin maganin bakteriya a Tanzaniya.
An yi amfani da hanyoyi mabambanta kamar (nazari, zuwa neman bayanai da tattaunawa).
An ziyarci gurare masu alaqa da binciken.
An sanar da rashin jin maganin penisilin G, kolorampinikol, sittamacin da kuma teterasakilin, musamman ma asinobakta payogins, staphilokakus hayikus, stapilokakus intamidus da stapilokakus awrus da ake samu daga shanun da ake tatsa da kuma mutane.
An kuma samo irin wannan matsalar cikin tsuntsaye inda kwai da nama ke dauke da nau’in eshirikia koli wanda ba ya jin maganin amozisilin + klabunet, sulpamezazol da nimaisin.
An kuma gano qaruwar sabon nau’in E. koli wanda ba ya jin magunguna dabam-dabam, kamar murar kilebsiyela, stapilokakus awrus da Salmonela.
An ruwaito qaruwar rashin jin maganin metisilin ga qwayoyin Stapilokakus awrus (MRSA) da nau’in qwayoyin cuta masu faxi (ESBL) cikin fannin dabbobi a Tanzaniya.
Qwayoyin da aka fitar daga dabbobi ba sa jin magungunan amfisilin, ogumentin, jentamasin, cotirimozol, teterasakilin, amosilin, sitirefromasin, nalidiksin asid, azitromasin, kuloramfinikol, tailosin, eritromasin, sifurosin, nofulozasin da sifurozasin.
An lura da qaruwar amfani da magungunan bakteriya kan frofilasis, da magungunan qwayoyin cuta da waxanda ke kara girman dabbobi, kayan noma da tsirrai.
An yi kira ga amfani da hanyar lafiya baixaya don yaqar rashin jin maganin bakteriya (AMR) cikin fannonin abinci da noma a Tanzaniya.
Shawarwarin aiwatarwa sun hada da (a) sake duba dokoki da aiwatar da su; (b) fahimtar da jama’a masu ma’amala da wannan fannin yadda ake amfani da magungunan bakteriya (AMU), AMR da burbudin magungunan bakteriya (AR); (c) karfafa ayyukan sa-ido da lura kan AMU, AMR da AR; (d) inganta ci gaba da amfani da hanyoyin gwaji nan-da-nan da yada tsaron kwayoyin halitta da (e) ayyukan kiwon dabbobi mai kyau.
Amfani da wadannan bayanai wajen inganta dokokin kula da lafiyar al’umma da rage barnar AMR yana da alfanu sosai.
Summary Title
Ingantattun xabi’u zai iya rage rashin jin magani ga qwayoyin bakteria ga magani a Tanzaniya.
Summary Body Text
Rashin jin maganin qwayoyin cutar bakteriya na da yawa ainun a Tanzaniya, kuma hakan na nufin magunguna ba sa warkar da mutane daga cututtukan da qwayoyin bakteriya ke haddasawa.
Masu bincike sun lura da abinda ke iya haddasa rashin jin maganin qwayoyin bakteriya kuma sun gano cewar dole sai an magance munanan xabi’u da ake da su a fannonin kayan abinci da noma domin rage rashin jin magani ga qwayoyin bakteriya.
Ana amfani da magungunan bakteriya sosai cikin abincin da ake samowa daga dabbobi kuma an yawaita ba da su ga marasa lafiya iri-iri, wanda hakan na iya rage musu qarfi.
Rashin jin maganin qwayoyin bakteriya matsala ce babba ga harka kiwon lafiya a duniya.
Ana iya alaqanta yawan amfani da maganin qwayar bakteriya a dabbobi ga makiyaya da kuma mutane masu lura da dabobbi waxanda ba su qware ba wajen amfani da waxannan magunguna don rashin cikakken ilimi.
Wannan binciken na nufin binciko ingancin dokokin gomnati kan amfani da maganin qwayoyin bakteriya a Tanzaniya.
Masu binciken sun kuma yi qoqarin gano yawan amfani da magungunan bakteriya ba bisa qa’ida ba ta hanyar lura da burbuxinsu cikin dabbobi da tsirrai.
Manufarsu shine ba da shawarwari kan hanyoyin magance rashin jin maganin bakteriya a qasar.
Masu binciken sun yi nazarin aiyukan da suka gabata, sun kuma kai ziyara guraren da ake amfani da magungunan bakteriya.
Sun kuma lura tare da tattaunawa da mutane 32, sun kuma yi zaman bahasi da makiyayan kaji 83.
Binciken ya gano cewar qwayoyin bakteriya sun daina jin magunguna kamar persilin G, kolorampinikol, sittamacin da kuma teterasakilin.
Ana amfani da waxannan muhimman magungunan bakteriya wajen warkar da qwayoyin cututtuka kamar Stapilokokus awrus wanda ke haddasa cutar nono mai zafin gaske ga mutane ko shanun da ake tatsa.
Sun kuma gano bayanai masu tsoratarwa kan dabbobi a Tanzaniya, kamar yawan rashin jin magani a bakteriya mai suna Esherikiya koli (E. koli), wanda ke haddasa ciwon hanji mai tsauri ko marar tsauri.
Masu bincike sun yi gargaxin cewa akwai matsalar yawan amfani da magungunan bakteriya cikin makiyaya don kariya ga dabbobi da kuma sa su girma da wuri.
Masu binciken sun ba da shawar cewa fannonin abinci da noma a Tanzaniya su yi amfani da hanyar kula da lafiya bai xaya (wato One Health) wanda ke lura da yanda mahalli, dabbobi da mutane ke tarayya wajen yaxa cuta don yaqar rashin jin maganin bakteriya.
Binciken ya ba da shawarar Tanzaniya ta sauya dokokin noma da hanyoyin aiwatar da su.
Masu binciken sun yi kira ga inganta xabi’un kiwo da kuma amfani da hanyoyin gwaji masu sauri don tabbatar da lafiya da tsaron dabbobi, ta yanda za a rage amfani da magungunan bakteriya ba bisa qa’ida ba.
This is Yoruba translation of DOI: https://www.mdpi.com/2079-6382/10/4/454#
This is Zulu translation of DOI: https://www.mdpi.com/2079-6382/10/4/454#
This is Northern Sotho translation of DOI: https://www.mdpi.com/2079-6382/10/4/454#
This is Amharic translation of DOI: https://www.mdpi.com/2079-6382/10/4/454#
This is Luganda translation of DOI: https://www.mdpi.com/2079-6382/10/4/454#