Description
Lay summary of the research article published under the DOI: 10.1101/2020.04.14.20064717
This is Hausa translation of DOI: 10.1101/2020.04.14.20064717
Haihuwar bakwaini shi ne haihuwa kafin cikar makonni 37.
An gudanar da wani bincike don kimanta alaƙar yawan jinin haihuwa da sinadarin saleniyam da jan ƙarfe da sinadarin zin da kuma haihuwar bakwaini.
Akwai mata 181 a cikin wannan binciken na musamman, 90/181 (49.7%) da 91/181 (50.3%) mata masu juna biyu kafin haihuwa.
Matsakaicin matsakaitan yawan ƙwayar sinadarin saleniyam shi ne 77.0; SD 19.4µg/L, jan ƙarfe ya kasance 2.50; SD 0.52 mg/L da kuma sinadarin zin ya kasance 0.77; SD 0.20 mg/L tare da waiwaye ga darajoji na 47-142µg/L, 0.76-1.59mg/L da kuma 0.59-1.11 mg/L, bi da bi.
Don haifuwar bakwaini, matsakaitan yawan ƙwayar sinadarin saleniyam shi ne 79.7; SD 21.6µg/L, jan ƙarfe ya kasance 2.61; SD 0.57 mg/L, kuma sinadarin zin ya kasance 0.81; SD 0.20 mg/L idan aka kwatanta da na lokacin haihuwa: Sinadarin saleniyam (74.2; SD 16.5µg/L; p=0.058), jan ƙarfe (2.39; SD 0.43 mg/L; p = 0.004), da kuma sinadarin zin (0.73; SD 0.19 mg/L; p = 0.006) bi da bi.
A cikin binciken da aka daidaita, kowane nau'i na ƙaruwa a cikin ƙananan ƙwayar sinadarin saleniyam na mahaifa ya ba da damar haɓakar kasancewa ko 1.01 (95% CI: 0.99; 1.03), p = 0.234, jan ƙarfe KO 1.62 (95% CI: 0.80; 3.32); p = 0.184, sinadarin zin KO 6.88 (95% CI: 1.25; 43.67); p=0.032.
Sakamakon ya nuna cewa babu ƙaranci na sinadarin saleniyam, da sinadarin zin; da yawan sinadarin jan ƙarfe a juna-biyu.
Haihuwar bakwaini yana da alaƙa da yawaitar adadin ƙwayar jan karfe da sinadarin zin.
Masu bincike sun gano yawan ma'adanai na sinadiran saleniyam da jan ƙarfe da kuma sinadari zin, a cikin matan da suka haifi bakwaini, amma har yanzu ba su san ko waɗannan abubuwan da ke tattare da su sun fito ne daga abincin da suke ci ba.
Haihuwar bakwaini na faruwa ne lokacin da mace ta haihu kafin ta cika makonni 37 na ciki.
Haihuwar bakwaini tana da alaƙa da mummunan sakamakon lafiya ga jariri tun daga lahani na haihuwa zuwa mutuwa.
Akwai dalilai da yawa na haifar da haihuwar bakwaini, amma ba a san rawar da yawan ma'adanai na abubuwan gina jiki da ake samu a abinci da muhalli suke takawa ba.
Waɗannan abubuwan gina jiki suna da mahimmanci ga ci gaban jariri, amma masu bincike suna so su san abin da zai faru idan akwai su da yawa.
Don wannan binciken, masu bincike sun yi niyyar auna adadin sinadarin saleniyam da jan ƙarfe da sinadarin zin a cikin matan da suka haifi bakwaini, sannan kuma don tantance rashin yiwuwar haihuwar bakwaini yana faruwa ne sakamakon yawan adadin kowane nau'in abubuwan gina jiki da aka nazarta.
Masu binciken sun tattara samfurin jini daga mata 181 kai-tsaye bayan sun haihu a asibitoci biyu a Lilongwe, babban birnin Malawi, tsakanin watan Yuni na shekarar 2016 da kuma Maris 2017.
Sun aika da samfuran jinin ne zuwa ɗakin gwaje-gwaje a ƙasar Norway inda suka fitar da ƙwayar jini, nau'in jini mafi kyau, kuma sun auna adadin sinadarin saleniyam da jan ƙarfe da kuma sinadarin zin.
Kimanin rabin mata 181 da aka gudanar da binciken a kan su sun haifi bakwaini, kuma masu bincike sun gano sinadarin saleniyam da jan ƙarfe da kuma sinadarin zin da yawa.
Daga nan sai suka daidaita lissafinsu don yin la’akari da wasu dalilai da yawa kamar shekaru da lafiya gabaɗaya da tarihin ciki don samun madogara game da zargin illolin da abubuwan gina jiki ke haifarwa na haihuwar bakwaini.
Sun yi ittifakin cewa yawan sinadarin saleniyam da jan ƙarfe ba sa taka muhimmiyar rawa wajen haifar da haihuwar bakwaini, amma yawan sinadarin zin na ƙara haɗarin haihuwar bakwaini da sama da sau 6.
Yawaitar jan ƙarfe duk da haka ya kasance damuwa ga masu bincike, saboda sakamakon da aka sani na guba.
Samun mata 181 kawai ne suka shiga cikin binciken ya iyakance ikon masu binciken don gano haɗarin da ke tattare da manyan matakan sinadarin saleniyam, kamar yadda adadin masu shiga binciken ya fi dacewa shi ne mata 600.
Ba a binciki abincin yau da kullum na masu shiga don gano hanyoyin da za a iya samun ma'adanai guda uku ba, kuma ba a rubuta Fihirisar Adadin Nauyin Jikinsu, Body Mass Index (BMI) ba.
Wannan shi ne nazari na farko da aka yi irinsa na auna tasirin sinadarin saleniyam da jan ƙarfe da kuma sinadarin zin ga mata masu juna biyu a Malawi.
Afirka tana da mafi girman matakan haihuwar bakwaini - sama da kashi 18% idan aka kwatanta da ƙasashen Yamma da kashi 5%, don haka masu bincike suna son sanin ko abinci mai gina jiki yana taka rawa.
This is Amharic translation of DOI: 10.1101/2020.04.14.20064717
This is Yoruba translation of DOI: 10.1101/2020.04.14.20064717
This is Zulu translation of DOI: 10.1101/2020.04.14.20064717
This is a Luganda translation of DOI: 10.1101/2020.04.14.20064717
This is a Northern Sotho translation of DOI: 10.1101/2020.04.14.20064717