Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Mutanen da ke dauke da kwayar cuta mai karya garkuwan jiki HIV a kan jiyya ba su da yuwuwar samun alamun cututtuka ko mutuwa daga COVID-19 fiye da yawan jama'a

Hausa translation of DOI: 10.1101/2020.06.04.20122606

Published onJun 17, 2023
Mutanen da ke dauke da kwayar cuta mai karya garkuwan jiki HIV a kan jiyya ba su da yuwuwar samun alamun cututtuka ko mutuwa daga COVID-19 fiye da yawan jama'a
·

Kamuwa da cutar COVID-19 da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki a lokaci guda: 

taswirar shaida mai rai na bincike na yanzu

A halin yanzu duniya tana fuskantar annoba guda biyu da ke ci gaba da lalacewa.

Waɗannan su ne sabbin cututtukan ƙwayar cuta na numfashi na coronavirus 2/cutar coronavirus 2019 (SARS-CoV-2/COVID-19) da ƙwayar cuta mai karya garkuwan jikin ɗan’adam/qanjamau (HIV/AIDS).

Rubuce-rubuce game da haɗuwar waɗannan annoba ta duniya suna faɗaɗa cikin sauri.

An yi tsararren binciken kan wallafe-wallafen da aka yi kan kamuwa da COVID-19 da cutar HIV.

Bayan watanni biyar, daga farkon cutar ta COVID-19, an sami aƙalla bincike talatin da biyar da aka ruwaito daga ƙasashe goma sha uku.

Waɗannan sun fito ne daga rahotannin na musamman da nazarin tsarin bincike mai gudana da yawa.

Dangane da binciken da za a iya keɓancewa ga yawan jama'a, mutanen da suke da ragaggen ƙwayar cutar HIV ba sa samun rashin lafiyar COVID-19 ko mutuwa na daban daga sauran mutane.

Aƙalla marasa lafiya huɗu, sabbin kamuwa da cutar HIV sun murmure daga cutar COVID-19.

Bayanai na yanzu sun nuna cewa ya kamata a kula da marasa lafiya da suka kamu da cutar kamar sauran jama'a.

Wannan taswirar shaida na rayuwa mai gudana na zamani na farko na SARS-CoV-2 da binciken haɗin ƙwiwar cutarr HIV yana ba da dandamali ga masu bincike, masu tsara manufofi, likitoci da sauran su don ganowa da haɓaka abubuwan da suka dace.


Mutanen da ke dauke da kwayar cuta mai karya garkuwan jiki HIV a kan jiyya ba su da yuwuwar samun alamun cututtuka ko mutuwa daga COVID-19 fiye da yawan jama'a

Yawancin bincike da aka yi a duniya sun nuna cewa mutanen da ke ɗauke da HIV/AIDS da ke kan jiyya ba sa fuskantar mummunan alamun COVID-19 ko sakamakonsa.

Masu binciken da suka sake nazarin binciken kimiyya na yanzu da ake samu kan wannan batun sun ce shaidar ta nuna ana iya kula da masu cutar HIV don COVID-19 kamar kowane mara lafiya.

Saboda mutanen da ke ɗauke da HIV sun raunana tsarin rigakafi, masu bincike sun damu cewa za su iya fama da rashin lafiya da mutuwa yayin cutar ta COVID-19.

Ta hanyar duban binciken mutum game da yadda masu cuta mai karya garkuwan jiki/qanjamau HIV/AIDS ke amsawa ga kamuwa da cutar COVID-19 da jiyya, masu binciken sun yi fatan zana gamayya don taimakawa sauran masu bincike, gwamnatoci da likitoci su yanke shawarar yadda za a bi da masu cutar HIV/AIDS waɗanda su ma suka kamu da COVID-19.

Sun bincika takaddun bincike masu ɗauke da kalmomi kamar "HIV", "AIDS", "Coronavirus" da "COVID-19", waɗanda aka saki tsakanin Janairu da Yuni, 2020.

Masu binciken suna neman takamaiman rahotanni game da masu ɗauke da HIV, ko mutanen da ke da HIV, waɗanda ke kan maganin rigakafin cutar AIDS kuma sun gwada ingancin COVID-19.

Daga binciken da suka yi, masu binciken sun gano takardu 35 daga kasashe 13, tare da bullar cutar COVID-19 na farko da cutar HIV a ƙasar Sin.

Sun gano cewa cuta mai karya garkuwan jiki/qanjamau HIV/AIDS kamar ba ya sa cutar ta COVID-19 ta yi muni, kuma sabbin masu cutar HIV da aka gano galibi sun murmure daga COVID-19.

Masu binciken sun kuma gano cewa majinyatan suna da alamun COVID-19 gama gari kamar tari, zazzavi, gajeriyar numfashi, gajiya, rasa jin wari da xanxano, da gudawa.

Majiyyaci xaya ne kawai ya kamu da daskarewar jiki.

Gabaɗaya, da alama mutane masu cuta mai karya garkuwar jiki/qanjamau HIV/AIDS suna kamuwa da COVID-19 kamar kowane mara lafiya.

Koyaya, haɗarin COVID-19 ya ƙaru ne kawai lokacin da marasa lafiya ke da wasu cututtuka kamar hauhawar jini, ciwon sukari, qiba da cutar qoda.

Masu binciken sun kuma bayar da rahoton cewa maganin cutar HIV/AIDS, darunavir, ba ya hana kamuwa da cutar Coronavirus.

Binciken nasu ya kuma nuna cewa majinyatan da suka kamu da cutar tare da dashen koda da hanta suma sun murmure daga COVID-19.

Masu binciken sun yi gargadin cewa ra'ayinsu na iya zama rashin son zuciya saboda kawai sun sami rubuce-rubucen da aka rubuta cikin Ingilishi.

Suna ba da shawarar ƙarin nazari kan yadda COVID-19 ke hulɗa da wasu cututtuka kamar tarin fuka, da ciwon huhu, da kuma yadda cututtukan haɗin gwiwa na iya shafar lafiyar kwakwalwar marasa lafiya.

Masu bincike daga Afirka ta Kudu ne suka tattara wannan bita, inda cuta mai karya garkuwar jiki/qanjamau HIV/AIDS ta kasance babban matsala ga kiwon lafiya.


Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?