Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Yan ƙasar Yuganda masu ɗauke da cutar HIV da hauhawar jini ba sa samun kulawar da suke buƙata

Hausa translation of DOI: 10.1186/s43058-020-00033-5

Published onOct 02, 2023
Yan ƙasar Yuganda masu ɗauke da cutar HIV da hauhawar jini ba sa samun kulawar da suke buƙata
·

Binciko shingaye da masu gudanarwa don haɗakar gudanarwar hauhawar jini-HIV a cikin asibitocin HIV na ƙasar Yuganda ta amfani da Ƙarfafa Tsarin Bincike don Aiwatarwa (CFIR)

ShimfiƊda

Mutane Masu Ɗauke da HIV (PLHIV) masu karɓar maganin rigakafi suna ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya (CVD).

An bayar da shawar haɗin ayyukan hauhawar jini (HTN), babban haɗarin da ke kawo Cututtukan Zuciya, a cikin asibitocin HIV a ƙasar Yuganda.

Ayyukanmu na baya sun nuna giɓi da yawa a cikin aiwatar da haɗin gwiwar kulawar HTN tare da maganin cutar HIV.

A cikin wannan binciken, mun nemi yin la’akari da shingaye da masu gudanarwa na haɗa gwajin HTN da magani zuwa asibitocin HIV a Gabashin ƙasar Yuganda.

Hanyoyi

Mun gudanar da bincike mai inganci a asibitoci guda uku masu cutar HIV tare da ƙarancin aiki da matsakaici da kuma babban aikin kulawar HTN, wanda muka rarraba bisa ga aikinmu na baya.

An jagorance shi ta Ƙarfafa Tsarin Bincike don Aiwatar (CFIR), mun gudanar da tsararrun tambayoyin tattaunawa da kuma tattaunawa ta rukuni tare da manajojin sabis na kiwon lafiya, masu kula da kiwon lafiya, da kuma Mutane Masu Ɗauke da HIV masu ɗauke da Hauhawar Jini (n = 83).

An rubuta tambayoyin tattaunawar a zahiri.

Masu bincike uku masu inganci sun yi amfani da hanyar cirewa (CFIR-driven) don samar da lambobi da jigogi masu dacewa.

An yi ƙididdiga don ƙididdige ƙima da ƙarfin kowane tsarin CFIR game da tasirin haɗin gwiwar HTN/HIV.

Sakamako

Matsalolin haɗin gwiwar HTN/HIV sun taso ne daga tsarin CFIR guda shida:

abubuwan ƙarfafawa da lada na ƙungiyoyi da albarkatun da ake da su da samun ilimi da bayanai da ilimi da imani game da kawo agaji da ƙwarewar kai, da kuma tsarawa.

Matsalolin sun haɗa da rashin injunan BP masu aiki, rashin isassun magunguna masu hana hauhawar jini da ƙarin nauyin aiki ga masu samar da sabis na HTN da ƙarancin ilimin kula da Mutane Masu Ɗauke da PLHIV game da kulawar HTN da ingantaccen ilimi da ƙwarewa da ingancin kai na masu ba da lafiya don dubawa da kula da HTN, da kuma rashin isassun tsare-tsare don haɗin gwiwar ayyukan HTN/HIV.

Dangantakar da take tattare da bayar da sabis na HTN da HIV a cikin cibiya-ɗaya, zai sauƙaƙa (rashin sarƙaƙiyar yanayi) na haɗaɗɗen kulawar HTN/ HIV, daidaitawa da dacewa da kulawar HTN tare da sabis cutar HIV da ake da su su ne masu haɓaka haɗin HTN/HIV.

Sauran tsare-tsaren CFIR ba su da mahimmanci game da tasirin haɗin Hauhawar Jini/HIV.

Kammalawa

Ta yin amfani da CFIR, mun nuna cewa yayin da akwai matsalolin da za a iya gyarawa zuwa haɗin HTN/HIV, haɗin HTN/HIV zai ba wa marasa lafiya da masu kula da lafiya da kuma manajoji sha’awa.

Haɓaka samun damar kulawar Hauhawar Jini a tsakanin Mutane Masu Ɗauke da HIV zai buƙaci shawo kan shingaye da yin amfani da masu gudanarwa ta amfani da tsarin ƙarfafa tsarin kiwon lafiya.

Waɗannan binciken sun kasance matattarar ƙirƙirar hanyoyin da suka dace don haɗakar HTN/HIV a cikin ƙananan ƙasashe da masu matsakaicin kuɗin shiga.


'Yan ƙasar Yuganda masu ɗauke da cutar HIV da hauhawar jini ba sa samun kulawar da suke buƙata

Bincike ya nuna cewa asibitocin HIV ba su da isassun kayan aiki da ma’aikatan da za su kula da majinyatan da su ma suke fama da hauhawar jini.

Hawan jini, ko hauhawar jini, yana shafar 1 a cikin manya 3 da suke zaune tare da cutar HIV a ƙasar Yuganda.

Tun da yake mutanen da suke fama da waɗannan yanayi guda biyu tare dole ne su yi tafiye-tafiye akai-akai zuwa asibitoci, masu binciken sun ce yana da ma’ana ga asibitocin HIV da ke da su su ma su gano tare da magance hawan jini, maimakon tura majinyatansu masu hauhawar jini zuwa wani wuri.

Abin takaici, yawancin asibitocin HIV ba su sami nasarar haɗa gwiwar kulawar hauhawar jini tare da cutar HIV da suka bayar ba.

Masu binciken sun binciki dalilin da yasa haɗin gwiwar kulawar ke aiki ko ba ya aiki a gabashin ƙasar Yuganda.

Fahimtar ƙalubalen zai taimaka wajen haɓaka ingantattun hanyoyi don haɗa gwiear kulawar hauhawar jini da kuma cutar HIV.

Sun yi hira da ma’aikatan kiwon lafiya a asibitocin HIV da kuma marasa lafiya da suke ɗauke da ƙwayar cutar HIV da kuma hauhawar jini.

Sun yi nazarin amsoshin ta amfani da daidaitattun hanyoyin kimiyya don inganta ayyukan kula da lafiya.

Sun gano cewa asibitocin HIV ba su da ƙwararrun ma’aikata da kayan aiki, gami da na’urorin hawan jini da kuma magunguna.

Har ila yau, marasa lafiya ba su san cewa za su iya samun kulawar likita ga cututtukan biyu a asibitocin HIV ba.

Wasu masu binciken sun yi nazarin yadda Afirka za ta iya haɗa kulawar hauhawar jini da kuma cutar HIV.

Duk da haka, wannan shi ne karo na farko da aka yi amfani da daidaitacciyar hanyar kimiyya da aka ambata a sama, wadda aka sani da Ƙarfafa Tsarin Bincike don Aiwatarwa (CFIR), don duba takamaiman hanyoyin magance matsalar.

Masu binciken sun yi gargaxin cewa a cikin binciken da suka yi, yawancin marasa lafiya ba su da masaniya game da haɗin gwiwar kulawar hauhawar jini da cutar HIV, saboda ba a taɓa shigar da su ba.

Wannan yana nufin cewa mutane da yawa ba za su iya amsa tambayoyin tattaunawa yadda ya kamata ba.

Don haka, sun ba da shawarar cewa ya kamata bincike na gaba ya mayar da hankali ne a kan ra’ayoyin marasa lafiya.

Sun kuma ce ana buƙatar ƙarin nazari don kwatanta farashi da fa'idojin haɗin gwiwar kulawar hauhawar jini da kuma cutar HIV.

Yuganda da sauran hukumomin kiwon lafiya na Afirka na iya amfani da fahimtar wannan bincike don tsara haɗin gwiwar kulawar hauhawar jini da kuma cutar HIV.

Da irin waɗannan ayyukan, za mu iya kawar da mutuwar da za a iya gujewa saboda hauhawar jini, tun da za a gano shi da wuri kuma a yi masa magani a lokacin da marasa lafiya suka nemi kulawa da cutar HIV.


Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?