Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Ma’aikatan kiwon lafiya, manyan likitocin da suka fi kamuwa da COVID-19

Hausa translation of DOI: 10.1101/2020.06.04.20119594

Published onMay 18, 2023
Ma’aikatan kiwon lafiya, manyan likitocin da suka fi kamuwa da COVID-19
·

Kamuwa da kuma Mace-mace na ma’aikatan kiwon lafiya a a faɗin duniya daga COVID-19: bita mai zurfi

Tsakure

 Manufa

Don kimanta kamuwa da COVID-19 da kuma mace-mace a cikin ma’aikatan kiwon lafiya (MKW) ta fuskar faɗin duniya.

 Tsari

Bita mai Zurfi.

Hanyoyi

 An gudanar da bincike guda biyu masu kama da juna na rumbun bayanai na littattafan ilimi da kuma na cibiyoyi waɗanda ba na ilimi ba.

Haka kuma an kuma tuntuɓi gwamnatoci don ƙarin bayani a inda ya dace.

Saboda yanayin lokacin bitar da kuma buƙatar bayar da rahoton sababbin bayanai don yanayi mai tasowa, babu ƙuntatawa a kan harshe da tushen bayanan da aka yi amfani da su da matsayin ɗab'i da kuma nau’o’in tushen shaida.

An yi amfani da bincika-jeri na AACODS don kimanta kowane tushen shaida.

Yanaye-yanayen wallafe-wallafe, wuraren musamman na bayanai na ƙasa, da bayanai na musamman na COVID-19 da ƙididdigar MKL da abin ya shafa, da kuma ma’aunan kiwon lafiyar jama’a da aka yi amfani da su.

Sakamako

 An bayar da rahoton adadin waɗanda suka kamu da cutar ya kai 152,888 sannan kuma 1413 sun mutu.

Cututtukan sun fi kasance a cikin mata (kashi 71.6%) da kuma ma’aikatan jinya (kashi 38.6%), amma yawancin mutuwar sun kasance a cikin maza (kashi 70.8%) da kuma likitoci (kashi 51.4%).

Taƙaitattun bayanan sun nuna cewa manyan likitoci da ma’aikatan aikin jinya sun kasance mafi girman haɗarin mutuwa.

An sami rahoton mutuwar mutane kashi 37.17 a cikin kashi 100 na kamuwa da cuta na ma’aikatan kiwon lafiya masu shekaru sama da 70.

Nahiyar Turai tana da mafi girman adadin kamuwa da aka ruwaito (119628) da kuma mace-mace (712), amma yankin Gabashin Bahar Rum ya fi yawan adadin mutuwar da aka bayar a cikin 100 na kamuwa da cuta (5.7).

Kammalawa

 Kamuwa da COVID-19 na MKL da mace-mace sun biyo bayan yawan al’ummar duniya.

Dalilan bambance-bambancen jinsi da na gwaninta suna buƙatar ƙarin bincike, kamar yadda aka ruwaito ƙima kaɗan daga Afirka da kuma Indiya.

Ko da yake ana iya ɗaukar likitocin da suke aiki a wasu fannonin ƙwarewa masu haɗari saboda hulɗa da yawu, amma bai kamata a ƙi la'akari da haɗarin da ke tattare da wasu a sauran fannonin ƙwarewa ba.

Ana iya saka tsofaffin MKL zuwa wurare masu ƙarancin haɗari kamar su kula da marasa lafiya ta hanyar sadarwa ko kuma matsayi na gudanarwa.

Hanyarmu ta la’akari a aikace ta bayar da yanayin abubuwan da suke faruwa gabaɗaya, kuma ta nuna buƙatun jagororin duniya don gwaji da bayar da rahoton kamuwa da cututtuka a cikin MKL.


Ma’aikatan kiwon lafiya, manyan likitocin da suka fi kamuwa da COVID-19

Ma’aikatan kiwon lafiya, manyan likitocin da suka fi kamuwa da COVID-19

 A cikin mummunar annobar COVID-19, ma'aikatan kiwon lafiya a duk faɗin duniya sun sanya rayukansu cikin haɗari wajen ceton wasu.

Wannan ne binciken farko da ya tantance yadda annobar ta yi illa ga ma’aikatan kiwon lafiya, da kuma ƙwararrun da suka fi fuskantar haɗarin kamuwa da cuta da kuma mutuwa.

 Daga wani gungun majinyata da suke da alamun ciwon huhu da suke da alaƙa da kasuwar sayar da nama ta Wuhan, China, a ƙarshen watan Disamba 2019, cutar koronabairas (COVID-19) ta rikiɗe da sauri zuwa wata cikakkiyar annoba ta duniya.

A lokacin gudanar da wannan binciken, wato watan Mayu na shekarar 2020, sama da mutane miliyan biyar ne suka kamu da cutar, kuma sama da mutane 300,000 sun mutu.

 A sahun gaba na wannan annoba ta duniya akwai ma’aikatan kiwon lafiya (MKL) waɗanda suke tantancewa da kuma kula da ɗimbin marasa lafiya da suke fama da matsananciyar rashin lafiya, waɗanda galibi suna yanke shawara mai mahimmanci a ƙarƙashin matsanancin matsin lamba na jiki da na hankali.

Wannan ya saka MKL cikin haɗarin kamuwa da cuta da kuma mutuwa, amma ba a san ainihin adadin waɗanda abin ya shafa ba.

Saboda haka, wannan binciken ya ƙiyasta ƙididdige adadin kamuwa da cutar COVID-19 a duniya da kuma batutuwan mutuwar MKL.

Masu binciken sun nemi bayanai a cikin takardun ilimi da gaurayen wasu tushe (wanda aka sani da wallafe-wallafen cibiyoyin da ba na ilimi ba), waɗanda suka haɗa da bayanan da gwamnati ta samar daga ko’ina a faɗin duniya da kafofin yaɗa labarai na yanar gizo, da kuma takardun da aka samar a shafin yanar gizo na medRxiv kafin wallafa su.

 Binciken ya gano cewa MKL guda 152 888 sun kamu da COVID-19, kuma guda 1413 sun mutu a sanadiyyar cutar.

Cututtukan sun fi kasance a cikin mata (kashi 71.6%) da kuma ma’aikatan jinya (kashi 38.6%), amma yawancin mutuwar sun kasance a cikin maza (kashi 70.8%) da kuma likitoci (kashi 51.4%).

A cikin bayanan da aka samu, binciken ya gano cewa manyan likitocin (ML) sun kasance cikin haɗarin mutuwa a tsakanin likitoci, a yayin da mafi girman haɗarin mutuwa a cikin ma’aikatan jinya shi ne a cikin sassan kula da lafiyar hankali.

A iya sanin masu binciken, wannan shi ne binciken farko don bincika kamuwa da cutar COVID-19 da kuma mutuwa a tsakanin MKL a faɗin duniya.

 Aikin nasu ya taƙaita ne da bayanan da ke akwai waɗanda suka haɗa da tushen bayanai masu yawa waɗanda suka sa ya zama da wahala a kwatanta su.

Haka nan ƙasashe daban-daban kuma sun kasance a matakai daban-daban na annobar a lokacin da suke tattara bayanai.

 Kamuwa da cutar COVID-19 da kuma mace-mace a cikin ma’aikatan kiwon lafiya sun biyo bayan yawan al’ummar duniya.

Dalilan bambance-bambancen jinsi da na gwaninta suna buƙatar ƙarin bincike, kamar yadda aka ruwaito ƙima kaɗan daga Afirka da kuma Indiya.


Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?