Description
Lay summary for the research article published under the DOI: 10.1007/978-3-030-36540-0_72
This is Hausa translation of DOI: DOI: 10.1007/978-3-030-36540-0_72
Rashin ilimi game da ma'adanai da kayan aikin ƙarfe na ma’adanan Mn matsala ce ta gama-gari a cikin samar da gamin ferromanganese.
Raguwa, wanda shi ne karyewar ɓarɓashi mai ƙarfi a kan ɗumama, muhimmin ma'aunin ingancin ma’adanan manganis ne wanda ba a yi nazari sosai ba.
Wannan aikin zai yi nazarin tasirin ma'auni daban-daban a kan ma'aunin raguwa lokacin da aka ɗumama ma’adanai a cikin murhu mai juyawa.
Waɗannan ma’aunai su ne saurin juyawa da yawan ɗumama da yanayi, da sinadarin da ke cikin ma'adinai.
Manufar takardar ita ce bayar da rahoto game da haɓaka hanyar.
Masu bincike sun gabatar da sabon gwaji don amsa tambayoyi game da kadarorin ma'adinan taman manganis da ake haƙowa a Afirka ta Kudu.
Masu bincike sun ba da shawarar wani sabon gwaji don gano ko wane yanayi ne na murhu zai iya rage rushewar manganis yayin samar da ƙarfe.
Wani muhimmin mataki na samar da ƙarafa shi ne raba manganis daga ma'adininsa ta hanyar ɗumama shi a cikin murhun da ake amfani da wutar lantarki.
Amma abin takaici, a lokacin irin wannan ɗumama manganis yana raguwa, ko kuma ya rushe zuwa ƙura, wanda zai iya sa tsarin ya yi rashin aiki kuma yana iya haifar da fashewa, saboda tarin iskar gas ta ciki.
Wannan binciken ya ba da shawarar sabuwar hanyar gwaji don ganin irin yanayin da zai iya rage raguwar taman manganis.
Masu binciken sun ba da shawarar gwada wannan ta hanyar yin amfani da nau’in murhun juyawa, wani nau'in murhu mai jujjuyawa, don ɗumama taman kafin a sarrafa shi a cikin tmurhu na wutar lantarki.
Masu binciken za su yi amfani da ma'adanai daga wuraren samun manganis na Kalahari na Afirka ta Kudu, kuma za su gwada yadda suke raguwa a cikin ɗakin gwaje-gwaje ta hanyar yin amfani da ƙaramin murhu mai juyawa.
Binciken zai gwada matakin raguwa a kan matakan juyawa da gudu daban-daban da yanayi da saurin ɗumama da girman ɓarɓashi na ma'adinai da da sinadarai na ma'adinai.
Masu binciken sun riga sun yi nazari na farko don tantance yiwuwar gwajin da aka tsara don samar da sakamako.
Sun sami sakamako mai ban sha'awa wanda ya nuna cewa lokacin da aka ɗumama ma’adinai na manganis daban-daban suna raguwa a yawa daban-daban dangane da sinadaransu.
This is Amharic translation of DOI: DOI: 10.1007/978-3-030-36540-0_72
This is Yoruba translation of DOI: DOI: 10.1007/978-3-030-36540-0_72
This is a Zulu translation of DOI: DOI: 10.1007/978-3-030-36540-0_72
This is a Northern Sotho translation of DOI: DOI: 10.1007/978-3-030-36540-0_72
This is Luganda translation of DOI: DOI: 10.1007/978-3-030-36540-0_72