Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Tsararren nazari kan magani da juriyar rigakafi na nau’ukan qwayar cutar hanta (HBV) a Afirka:Kira ga matakin gaggawa

This is Hausa translation of DOI: 10.1371/journal.pntd.0006629

Published onJul 24, 2023
Tsararren nazari kan magani da juriyar rigakafi na nau’ukan qwayar cutar hanta (HBV) a Afirka:Kira ga matakin gaggawa
·

Tsararren nazari kan magani da juriyar rigakafi na nau’ukan qwayar cutar hanta (HBV) a Afirka:Kira ga matakin gaggawa

Tsakure

Muradu masu xorewa na qasa da qasa kan kawar da qwayar cutar hanta da kuma tabbatar da ta daina zama matsala ga kiwon lafiya kafin shekar 2030 ya nuna buqatar havaka hanyoyin kariya, jinya da warkarwa.

Na’uka masu alaqa da juriyar magani (RAMs) da juriyar rigakafi (VEMs) na qwayar cutar hanta (HBV) na iya rage nasarar hanyoyin magani da kariyar da ake da su a yanzu.

Waxannan abubuwa na da muhimmanci musamman ga kevavvun yanayi a Afirka inda ake da yawan yaxuwar HBV game da HIV a baixaya, ga kuma rashin wadataccen bayanai kan qwayoyin cuta masu saurin yaxuwa da qarancin ilimi, jinya da kula.

Ba a kula da yaxuwa, rarrabuwa da qarfin RAMs da VEMs cikin rubuce-rubuce da ake da su a yanzu.

Shi ya sa muka haxa bayanai kan qasashen baqaqe na Afirka ta hanyar tsararren bita da nazarin bayanai suke cikin aiyukan da suka gabata waxanda aka wallafa, da kuma gabatar da su a kundin bayanai na intanet (https://livedataoxford.shinyapps.io/1510659619-3Xkoe2NKkKJ7Drg/).

Yawancin bayanan an samo su ne daga guraben masu xauke da HIV/HBV a lokaci guda.

RAM da aka fi samu shi ne rtM204I/V, ko shi kaxai ko haxe da nau’uka masu alaqa da shi, wanda aka samu cikin mutanen da suka tava shan magani da waxanda basu tava ba.

Mun kuma gano jerin nau’uka rtM204V/I + rtL180M + rtV173L, wanda yake da alaqa da juriyar rigakafi ciki 1/3 guraben mutane da aka yi bincike a kansu.

Ko da yake, tenopobir, yana da qarfin kariya daga rashin amfa ga qwayar cuta mara jin magani, matsala ne a samu bayanai masu nuni da cewar folimofis na da alaqa da rashin jin magani, duk da cewar ba san cikakken bayani ba a yanzu.

Duka-duka dai, akwai buqatar gaugawa na ingantaccen gwaji, qarfafan duba sakamakon gwajin HBV kafin da kuma bayan jinya, da wadataccen samun tenopobir fiye da samun lamibudin kawai.

Ana buqatar qarin bayanai don fahimtar da al’umma da xaixaikun mutane hanyoyin ganowa, kula da jinyar HBV a wannan yanaye-yanaye masu haxari.

Summary Title

Rashin jin magani da juriyar rigakafi na HBV matsalar gaugawa ce ga Afirka

Summary Body Text

Afirka na da yawan yaxuwar qwayar cutar hanta (HBV) marasa jin magani da juriyar rigakafi, wanda ya ke barazana ga kiwon lafiya a wannan nahiya mai fama da cutar HIV.

Masu bincike sun ce dole Afirka ta saka jari sosai ka samar da magunguna da hanyoyin warkar da HBV.

Muradun Ci Gaba mai xorwa na Majalisar Xinkin Duniya (SDG 3) na kira ga qarar da bazanar da qwayar cutar hanta ke yi wa kiwon lafiyar al’umma kafin 2030.

Wannan na nufin inganta hanyoyin kare kamuwa, magani da jinyar qwayar cutar hanta.

Sai dai, waxansu nau’ukan qwayar cutar hanta mai alamar B (HBV) na kawo cikas wajen koqarin kare kamuwa da jinyar cutar.

Akwai waxannan matsalolin a Afirka inda ke da yawa yaxuwar HBV game da HIV a lokaci guda.

Kuma akwai qarancin bayanai kan yaxuwa da karfin nau’ukan da ke sa HBV ya zama ba ya jin magani ko ya jure garkuwar jiki wanda ake samu daga rigakafi.

A wannan bincike, masu bincike sun yi bitar y’an bayanai da ake da su a kasashen baqaken Afirka suka kuma wallafasu a kundin intanet guda xaya.

Kundin ya kwatanta yawa, yaxuwa, da faruwar nau’uka da suke da alaqa da qwayoyin HBV marasa jin magani (RAMs) da masu juriyar rigakafi (VEMs) a Afirka.

Masu binciken sun bubi rubuce-rubuce a kundayen kimiyya na MEDLINE, SCOPUS, da EMBASE tsakanin Oktoba 2017 da Janairu 2018.

Daga wxannan aiyukan, sun taskace shekarar wallafawa, tsarin bincike, yawan misalai, al’ummar bincike, magunguna da wasu muhimman bayanai da aka samu akan ko wane wallafaffen aiki.

Sun gano cewar nau’in da ya fi alaqa da rashin jin magani a Afirka shi ne rtM204I/V, wanda aka samu cikin mutanen da suka tava shan magani da waxanda bas u tava sha ba.

Binciken ya gano cewar rtM204V/I, rtL180M, da rtV173L, wanda ke da alaqa da juriyar rigakafi na iya samuwa cikin kaso uku na guraben mutanen da aka yi amfani da su wajen bincike.

Masu binciken sun nuna cewar maganin nan mai suna tenopobir yana da alamar haddasa juriyar magani, duk dai ba a san hakan ba a baya.

Sakamakon ya nuna yawaitar waxannan nau’ukan a wadu al’ummu na qasahen baqar fata a Afirka.

Rashin kayan aiki ya taimaka wajen rashin samun gwajin HBV, rashin wanzuwar magani, da rashin samun ingantacen jinya da kula, waxanda ababe ne da suke taimakawa wajen sa cuta ta qi jin magani ko ta juri rigakafi.

Wannan ita ce bita ta farko da ta dubi RAMs da VEMs na HBV a Afirka.

Yawan kamuwa da HBV cikin mutane masu xauke da HIV a wasu gurare da suka haxa da Kamaru da Afirka ta Kudu manuniya ce cewar kamuwa da HBV abu ne da ba a ruwaitowa sosai a baya, qila saboda rashin gwaji, qarancin wayewar kai, qyama, da tsada da qarancin kayan jinya da gwaji.

Ba a gudanar da gwajin cutar HBV a da yawan yanayi a Afirka wanda ke sa ba za a iya sanin gaskiyar yawan yaxuwa da yanaye-yanayen cutar HBV.

Masu binciken sun iya gano y’an kaxan a aiyukan da aka wallafa na masu xauke da HBV wanda ke da alaqa da yanayin qwayar halitta.

Wannan ya nuna rashin ko inkula kan matsalar HBV a Afirka, da givin sani a kan bayanai na qwayar halitta.

Bisa sakamakon wannan binciken, masu bincike sun ba da shawarar zuba jari mai xorewa don faxaxa samun magani da rigakafi, da bada gwaji don gano cutar da kuma hango yiwuwar qeqeshewa na rashin jin magani.

Ana buqatar qarin bayanai don fahimtar da al’umma da xaixaikun mutane hanyoyin ganowa, kula da jinyar HBV a wannan yankin qasashen baqaqe a Afirka mai cike da haxarin kamuwa da cutar.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?