Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Waɗanda suka rasa gaɓoɓi a yaƙin basasar Uganda har yanzu suna nan ba tare da taimako ba

Hausa translation of DOI: 10.1101/2020.05.14.095836

Published onMay 24, 2023
Waɗanda suka rasa gaɓoɓi a yaƙin basasar Uganda har yanzu suna nan ba tare da taimako ba
·

Nazarin Wakilcin Yawan Jama’a na Yaɗuwa da Yanayin Babbar Asarar Gaɓoɓi a Ƙaramin Yankin Acholi na Ƙasar Uganda

Tsakure

SHIMFIƊDA

 Akwai rahotannin da ke yaɗuwa game da babbar asarar gaɓoɓi a Arewacin Uganda, wanda aka yi imanin cewa ya faru ne a babbar ɓangare sanadiyyar yaƙin basasa da aka daɗe ana yi.

Samun wuraren gyara yana da iyaka sosai, kuma ba a taɓa yin wani bincike don fahimtar mutane nawa ne suke da babbar asarar gaɓoɓin ba, ko nawa ne daga cikinsu suka sami damar taimakon likita ko ayyukan gyarawa.

MANUFA

Nazarin yawitar nakasa na farko da kuma babbar asarar gaɓoɓi a cikin yankin, da kuma kimanta yanayin faruwar BAG.

TSARI

Nazarin wakilcin yawan jama’a.

WURI

An gudanar da wannan binciken ne a cikin yanayin al’umma (a gidajen masu larurar).

YAWAN JAMA’A

Gidaje 7,864 da aka zaɓa kara-zube a ko’ina cikin Ƙaramin Yankin Acholi na Arewacin ƙasar Uganda.

HANYOYI

 Wannan binciken ya ƙunshi takardar jerin tambayoyi guda biyu, magidanci na kowane gida da aka ɗauki samfur ne zai (n=7,864), ta biyu kuma ta kowane ɗan gida na gidan da ke da babbar asarar gaɓoɓi (n=181).

An bincika wuraren gida don daidaitawar yanayin danganta ta kai-tsaye ta amfani da ƙididdigar I na Moran.

An yi amfani da ƙididdigar kyawun dacewa na X^2 don yin bayanin waɗanda ke da babbar asarar gaɓoɓi idan aka kwatanta da yawan jama'a.

SAKAMAKO

 Mun la'akari a hankali cewa akwai mutane c.10,117 da ke da babbar asarar gaɓoɓi a yankin waɗanda ke buƙatar ayyuka na gyare-gyare na dogon lokaci (kashi c.0.5% na yawan jama'a), da kuma c.150,512 mutanen da ke da nakasa ban da BAG (kashi c.8.2% na yawan jama'a).

Mutanen da ke da babbar asarar gaɓoɓi sun bazu a ko’ina cikin yankin (saɓanin taruwa a takamaimun wurare) kuma sun fi yawa ga mazaje tsofaffi, kuma masu ƙarancin ilimi fiye da sauran jama'a.

KAMMALAWA

 Wannan bincike ya nuna cewa, a karon farko, girman rashin isassun ayyuka na gyare-gyare na dogon lokaci ga waɗanda suke da babbar asarar gaɓoɓi a yankin binciken.

Muna bayar da sabon haske game da dalilan da mutane ba sa samun damar yin amfani da ayyuka na kiwon lafiya da na gyarawa, kuma muna ba da shawarar wata hanya ta ci gaba ta hanyar nasarar nunin samfurin ‘asibitin na musamman’.

TASIRIN GYARAWAR ASIBITI

Gano yanayin na waɗanda ke da babbar asarar gaɓoɓi, tare da nunin samfurin isar da asibiti na musamman, yana ba da hujja mai ƙarfi don buƙatar ƙarin irin waɗannan ayyuka da tsare-tsare masu alaƙa a yankuna masu nisa da kuma karkara a Kudancin Duniya.


Waɗanda suka rasa gaɓoɓi a yaƙin basasar Uganda har yanzu suna nan ba tare da taimako ba

 A karon farko, masu bincike sun binciki mutanen da ke fama babbar asarar gaɓoɓi (BAG) da sauran nakasa a Ƙaramin Yankin Acholi da ke Arewacin ƙasar Uganda.

Masu binciken suna fatan gwamnati da sauran ƙungiyoyi za su iya amfani da bayanan don ba da ayyuka na asibiti a inda mutane suka fi buƙata.

 Ƙaramin Yankin Acholi da ke Arewacin ƙasar Uganda ya sha fama da yaƙin basasa na tsawon shekaru 20 wanda ya ƙare a shekara ta 2005.

Mutane da yawa sun rasa gaɓoɓi a sanadiyyar yaƙin, kuma yankin ya kasance cikin talauci.

Abin takaici, har ya zuwa yanzu gwamnatin ƙasar da ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasa-da-ƙasa ba su san takamaimai yawan mutanen da ke da nakasa da suke da damar samun taimakon likita ko wajen kulawa a wannan yanki ba.

 Wannan shi ne binciken farko don bincika yadda BAG ke yaɗuwa a Ƙaramin Yankin Acholi.

Manufar wannan bincike ita ce gano nau’o’in nakasa daban-daban da kuma babbar asarar gaɓoɓi da ake samu a cikin al’ummar wannan yanki a Arewacin ƙasar Uganda, da kuma samarwa gwamnati da sauran ƙungiyoyi taswirar wuraren da aka fi buƙatar cibiyoyin kiwon lafiya.

 Masu binciken sun tattauna da mutane 7864 a cikin zaɓaɓɓun gidaje kara-zube a cikin yankin binciken inda suka tambayi shugabannin kowane gida da kuma mutane 181 masu BAG don amsa ɗaya daga cikin takardar jerin tambayoyin biyu.

Sun ɗauki bayanin wurin kowane gida kuma sun yi amfani da hanyar ƙididdigar I na Moran don tantance inda BAG ya fi yawa da kuma inda za a buƙaci mafi yawan ayyuka.

 Tun da ya kasance masu binciken ba za su iya ziyartar kowane gida a yankin ba, suna buƙatar samfurin gidajen da za su wakilci ragowar jama'a.

Sun yi amfani da hanyar ƙididdiga da ake kira “kyawun dacewa Chi-squared (X^2)” don tabbatar da cewa gidaje tare da mutanen da ke da BAG suna wakiltar ragowar jama'a.

 Masu binciken sun ƙididdige cewa kusan kashi 0.5% na yawan jama'a suna da BAG kuma suna buƙatar ayyuka na gyarawa na lokaci mai tsawo.

Haka nan kuma sun gano cewa kusan kashi 8.2% na mutanen da ke zaune a can suna da wasu nakasa.

 Binciken ya nuna cewa mutanen da ke da BAG suna yaɗuwa a ko’ina cikin yankin kuma ba a tattara su a wasu yankuna kaɗan na musamman ba.

Yawancin mutanen da ke da BAG sun kasance maza tsofaffi, kuma suna da ƙananan matakan ilimi idan aka kwatanta da sauran jama'a.

Waɗannan sakamakon su ne na farko da aka yi ƙiyasin yadda BAG ke yaɗuwa a Ƙaramin Yankin na Acholi, duk da cewa rikicin ya kawo ƙarshe sama da shekaru 15 da suka gabata.

Abin takaici, masu bincike sun dogara ne da bayanan ƙidayar jama’a da ya wuce shekaru 5, kuma ba su da alƙaluma na ƙaruwar yawan ‘yan gudun hijira.

 Duk da wannan gazawar, wannan binciken har yanzu ya nuna cewa ayyukan gyare-gyare a ƙaramin yankin Acholi sun kasa taimakawa mutane da yawa da suke fama da babbar asarar gaɓoɓi.

Masu binciken sun ba da shawarar sabon tsarin isar da asibiti wanda ke sanar da gwamnati da ƙungiyoyin sa-kai na ƙasa-da-ƙasa game da inda ayyukan gyaransu zai zama mafi taimako.

Haka nan kuma sun ce akwai yiyuwar ana buƙatar ayyukan gyara a wasu yankunan karkara da yaƙi ya ɗaiɗaita a Kudancin Duniya.


Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?