Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Tashin hankali ya yi hasashen ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo

Hausa translation of DOI:

Published onMay 18, 2023
Tashin hankali ya yi hasashen ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo
·

Samfurin keɓaɓɓun bayanai na Bayes kan ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo ta hanyar INLA-SPDE

Tsakure

 Ƙwayar cutar Ebola (EBV) ita ce cutar da duniya ta amince da ita ta bullowa lafiyar jama'a, wadda take keɓaɓɓiyar annoba a Yammacin Afirka da yankin ekwatoriya.

Domin fahimtar yaɗuwar cuta, musamman cutar cutar EBV masu sauyawa, muna nazarin bayanan sanarwar EBV don tabbatar da faruwar da aka bayar da kuma rahoton mutuwa na ɓarkewar cutar a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo (DRC) a tsakanin shekarar 2018 da 2019, kuma mun bincika tasirin tashin hankali da aka ruwaito na yaɗuwar ƙwayar cutar.

Ta yin amfani da cikakken binciken ƙididdiga ta hanyar keɓaɓɓun bayanai na Bayes ta hanyar daidaitattun daidaiton ɓangarori na stochastic (SPDE) wanda suke ba mu damar ƙididdige tsarin keɓaɓɓun bayanai a kowane wuri a keɓaɓɓen yanki.

An dangane ƙimar ma'auni ne dangane da integrated nested Laplace approximation (INLA).

Abubuwan da bincikenmu ya gano sun nuna ƙaƙƙarfar alaƙa a tsakanin tashin hankula a yankunan da abin ya shafa da kuma rahoton EBV da mutuwar mutane, da kasancewar gungu na da mace-mace duka biyun sun bazu zuwa maƙwabta a cikin ɗabi’a iri ɗaya.

Sakamakon binciken yana da amfani don gano wuri da ta addabi mutane da sa-ido na musamman ga keɓaɓɓun wuraren cututtukan da kuma kawo ɗauki.

Tasiri a shekarar 2018, Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo (DRC) ta tabbatar da ɓullar annobar cutar Ebola karo na goma a cikin shekaru 40.

Ɓarkewar ita ce ɓarkewar cutar Ebola mafi girma a ƙasar kuma ta biyu mafi girma da aka taɓa samu bayan ɓarkewar cutar ta Yammacin Afirka a tsakanin shekarar 2014-2016.

An bayar da rahoton ɓullar cutar a halin yanzu a yankin da aka daɗe ana rikici, wannan binciken ya mayar da hankali ne a kan binciken yadda cutar Ebola take yaɗuwa a DRC da kuma rawar da tashe-tashen hankula suke takawa.

An kuma gano abubuwan da suka faru na tashin hankali a yankunan da abin ya shafa suna da alaƙa da rahotannin ɓullar cutar Ebola, wanda yake da matuƙar dacewa don gano wurin da cutar ta addabi mutane da kuma sa-ido kan wuri na musamman da na cutar da kuma kawo ɗauki.


Tashin hankali ya yi hasashen ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo

Tashin hankali ya yi hasashen ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo

 Ƙwayar cutar Ebola (EBV) cuta ce mai saurin yaɗuwa, cuta ce wacce wadda ta fi muni sanadiyyar tashe-tashen hankula a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo (DRC).

Masu bincike yanzu suna iya yin hasashen inda ɓarkewar EBV za ta faru ta amfani da bayanai daga abubuwa na tashin hankali.

 Cutar Ebola ta zama keɓaɓɓiyar annoba ta gaggawa ta lafiyar jama’a da aka amince da ita a ƙasashen Yamma da yankin ekwatoriya na Afirka.

Ɓarkewar baya-bayan nan a DRC ita ce ta biyu mafi girma da aka taɓa samu a Yammacin Afirka.

A wannan ƙasa, rikice-rikice na masu ɗauke da makamai suna samar da yanayi mai kyau ga cututtuka bijirowa da kuma yaɗuwa, saboda an lalata kayayyakin more rayuwa da kayayyakin kiwon lafiya, kuma mutane da yawa sun yi hijira.

A cikin wannan binciken, masu binciken sun nemo alaƙa da take tsakanin yaɗuwar cutar Ebola da kuma yankunan da aka samu rahoton tashin hankali a DRC a cikin shekarar 2018 da 2019.

 Masu binciken sun yi amfani ne da hanyoyin ƙididdiga bisa ra’in Bayes, wanda yake amfani da ƙananan bayanai don hasashen lokacin ko inda wani lamari zai faru.

Masu binciken sun yi amfani da bayanai na musamman game da ɓarkewar tashin hankali a wasu yankuna don hasashen inda cutar Ebola za ta iya ɓulla a nan gaba.

 Binciken ya gano cewa yankunan da tashe-tashen hankulan suka shafa suna da alaƙa sosai da rahotannin kamuwa da cutar Ebola da kuma mace-mace, waɗanda suka bazu zuwa yankunan da suke maƙwabtaka da su.

Masu binciken sun kuma ba da rahoton ɓullar cutar Ebola da mace-mace a inda ba a tattara bayanai ba saboda tashe-tashen hankula da ake ci gaba da yi.

A karon farko a DRC, wannan binciken ya nuna cewa za a iya amfani da Samfurin keɓaɓɓun bayanai na Bayes don gano wuraren da cutar ta Ebola ta addabi mutane inda ba za a iya samun bayanai ba.

 Duk da haka, masu binciken ba za su iya bambanta tsakanin nau’o’in abubuwan tashin hankali ba da kuma yadda suke tasiri musamman wajen tsarin kula da lafiya a wuraren da abin ya shafa.

Masu binciken har ila yau ba su tattara bayanansu a kan abubuwan da suka faru na tashin hankali ta hanyar da za su iya yin hasashen ainihin lokacin da ɓarkewar cutar Ebola za ta faru ba.

Masu binciken sun ba da shawarar cewa hukumomi a DRC su samar da tsauraran matakan sa-ido a kan cututtuka da kuma ɗaukar mataki a yankunan da abin ya shafa, da ma a dukkan sassan ƙasar don inganta ganowa da shawo kan cutar da wuri don daƙile yaɗuwar cutar Ebola.


Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?