Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Sabon Tsarin Fabrin Faiba a Ciwon Gavvai da Alaqarsa da Sava Tsarin Garkuwar Jiki, Kumburi da Daskarewar Jini

This is Hausa translation of DOI: 10.1101/2020.05.28.121301

Published onJul 24, 2023
Sabon Tsarin Fabrin Faiba a Ciwon Gavvai da Alaqarsa da Sava Tsarin Garkuwar Jiki, Kumburi da Daskarewar Jini
·

Sabon Tsarin Fabrin Faiba a Ciwon Gavvai da Alaqarsa da Sava Tsarin Garkuwar Jiki, Kumburi da Daskarewar Jini

Tsakure

Muradai:

Hadarin ciwon zuciya a cikin marasa lafiya masu fama da RA yana karuwa sosai saboda kumburi.

Zuwa yanzu, ba a san tasirin tsarin garkuwar jiki kan tsarin fabrins ba.

Saboda haka muka kwatanta aikin hanyoyin jini, kumburi, daskarewa da dunqulewar jini cikin marasa lafiya masu RA da kevavvun hanyoyin lura da alaqar da ke tsakani.

Hanyoyi.

A kavi samfurin jini daga marasa lafiya masu RA 30 da masu gudummowar sa kai 25 waxanda aka raba bisa shekaru da jinsi.

An gwada matakan SAA, CRP, ICAM-1 da VCAM-1 ta hanyar rarrabe sinadaran kariyar jiki.

An gwada daskarewar jini ta hanyar turombolastogifi.

An binciki hanyoyin fabrin da tsarin fayba ta hanyar amfani na’urar gwajin sinadarai.

An yi amfani da tsarin Sitrulin wajen ganowa da awon yanayin dungulewar jini cikin dungulallen fabrin.

Sakamako.

Taruwar SAA, CRP da ICAM-1 ya fi yawa cikin masu RA kan waxanda ba su da shi.

Hanyoyin TEG da suke da alaqa da soma daskara (R and K), yawan cakuxar fabrin (α-Angle), da lokacin ya ke xauka kafin daskarewar jini sun ragu cikin marasa lafiya masu RA.

Ba a samu bambamcin qiyasi ba cikin abubuwa masu alaqa da qarfin dunqulellen jini (MA, MRTG, TGG) tsakani masu RA da waxanda ba su da shi.

Ilimin bambanta abubuwa ya nuna alaqa mai qarfi tsakanin farkon cuta da abubuwa masu nuna ingancin sinadarai masu daidaita garkuwar jiki.

Gwajin na’urar awo ya nuna karfin tsarin fabrin cikin masu RA kan waxanda ba su da shi 214 (170-285) kan 120 (100-144) nm, p<0.0001, resho =22.7).

Gano guraben sauye-sauyen sinadarai cikin dunqulallen fabrin na masu RA, wanda bai kai yawan na marasa ba (p<0.05, ko =2.2).

Kammalawa.

Masu cutar RA na nuna samun alamar dunqulewar jini wanda ya sava da sakamakon bincike kan yanayin wasu kumburin.

Canja yanayin sinadarin protin ta hanyar sauyawar garkuwar jiki na iya taimakawa wajen yanayin fabrin da qaruwar dungulewar jinin cikin jijiya ga masu RA.

Summary Title

Dungulewar jinni cikin masu ciwon gavvai manuniya ce kan yanda suke iya kamuwa da bugun zuciya da garsa

Sabon bincike kan ciwon gaba ya qara baiyanar da fahimta kan yiwuwar alaqa tsakanin cutar da haxarin kamuwa da ciwon zuciya.

Ciwon gaba (RA) ciwo ne mai zafi da tsanani sosai wanda ke faruwa indan garkuwan jiki ya sava tsari, kuma yana da alaqa da kumburi a duk gavvan jiki.

Da daxewa masana kimiyya sun san cewa 50% na masu wannan cutar na iya kamuwa da cutar zuciya (CVD) mai haddasa garsa da bugun zuciya.

Hatsarin da ya fi girma shi ne alaqar kumburi da hanyar dunqulewar jini.

A wannan binciken, masu bincike sun zaqulo wannan alaqar, don gano takamammen abin da ya sa RA ke qara haxarin CVD.

A taqaice dai, masu binciken sun gwada illar kumburi da canjin tsarin protin da ke da alaqa da dunqulewar jini wanda ake kira fibrins.

Waxannan sinadaran protin na faruwa ne kamar dogon layi mai sarqe da juma, saboda haka canjawar fabirins xin na iya shafar hanyoyin dunqulewar jini kai tsaye.

Masu bincike sun kwatatanta jinin marasa lafiya masu RA da na mutane masu lafiya.

A ko wane yanayi, masu binciken na neman alamu cikin jini waxanda suke nuna kumburi, da dukkan bambamce-bambamce da cikin hanyoyin dunqulewar jiki da zai qara hatsarin CVD.

An gwada dunqulallen jinin ta hanyar na’urar gwaji, don gano sauye-sauye cikin tsarin protin nau’in fabrin.

Masanan sun lura da cewa jin marasa lafiya masu RA ya fi saurin dunqulewa a kan na masu lafiya, kuma irin sinadaran protin da aka yi su da su ya fi na fabrins da aka sani kawri.

Akwai kuma sauye-sauyen animo asid da aka yi fabrin xin da su, wanda ke haddasa tashin farkuwar jiki, wanda hakan na jawo qaruwar kumburi.

Kafin wannan binciken, wasu masu bincike sun lura da sauye-sauyen yanayin amino asid na fabrins a gavaven marasa lafiya masu RA, amma wannan ne karo ne farko na farko da masu bincike suka ga tasiri mai kama da juna cikin jini.

Haxe da wasu sauye-sauye da aka gani cikin dunqulallen jini, sakamakon zai taimaka wa masana kimiyya wajen samun cikakken fahimtar alaqa tsakanin RA da CVD, da yanda za a gane alamun waxannan cutuka da wuri.

Duk da cewar wannan sakamakon na da alfanu, ya kamata a sani cewa yawan abin bincike da aka yi amfani da su kaxan ne idan aka kwatanta shi wasu binciken.

Kuma masu binciken sun ce ta iya yiwuwa hanyoyin bincike da suka yi amfani da su wajen gano sauye-sauyen amino asid cikin sinadaran protin ya xauko wasu abubuwa da ba su da alaqa, wanda hakan na nufin ana buqatar qarin gwaje-gwaje na musamman kan fabrins don tabbatar da wannan sakamakon nan gaba.

Zuwa gaba, fahimtar cakuxaxxar alaqa tsakanin RA da yawaitar haxarin CVD zai kyautata samun sauqi ga marasa lafiya masu RA tunda muna koyon ganowa da magance waxannnan cutuka.

Masu bincike daga Afirka ta Kudu, Denmak da Ingila na cikin masu binciken nan, wanda Qungiyar Bincike kan Magani ta Afirka ta Kudu ta xauki nauyinsa.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?