Description
This is a lay summary for the article published under the DOI: 10.1186/s12891-020-03341-y
Hausa translation of DOI: 10.1186/s12891-020-03341-y
Ma’aikatan jinya a Afirka tabbas su ne mafi mahimmancin ma’aikatan kiwon lafiya na sahun gaba da ake samu a yawancin wuraren kiwon lafiya, suna yin ayyuka da yawa.
Ana ɗaukar Irin waɗannan ayyuka a cikin sanadin nauyin aiki.
An jera aikin ma’aikatan jinya a cikin sana’o’i mafi haɗari wajen samar da ciwon ƙasan baya.
Aikin jinya yana cikin manyan sana’o’i guda goma waɗanda ke da babban haɗari na ciwon ƙasan baya.
Domin haka, wannan bita na nufin tabbatar da ko ciwon ƙasan baya yana da matuƙar damuwa ga ma’aikatan jinya a wuraren kiwon lafiya na Afirka.
An gudanar da cikakken binciken wallafe-wallafe na rumbunan adana bayanai daban-daban ba tare da iyakance kwanan wata ba daga watan Satumba zuwa na Nuwamba 2018 ta amfani da jagorar PRISMA.
An kimanta ingancin karatun da aka haɗa ta amfani da tsarin ƙididdige abu-12.
An aiwatr da nazarin ƙaramin-rukuni da kuma hankali.
An yi amfani da Cochran's Q da gwajin I2 don tantance bambance-bamancen yanayin.
An ƙididdige kasancewar son rai na ɗab’i ta hanyar amfani da gwajin Egger da duban gani na daidaito a cikin ma’aunin mazurari.
A cikin wannan bita, an haɗa bincike guda19 daga yankuna daban-daban na Afirka tare da girman samfurin adadin ma’aikatan jinya 6110.
An gudanar da duk binciken ne a tsakanin shekara ta 2000 zuwa ta 2018.
Daga cikin waɗannan, an gano mafi ƙanƙanta kuma mafi girma su ne kashi 44.1 da kashi 82.7% bi-da-bi.
An gano ƙididdiga na yawan ciwon ƙasan baya a tsakanin ma’aikatan jinya ta amfani da samfurin bazuwar sakamako shi ne kashi 64.07% (95% CI: 58.68–69.46; P-value < 0.0001).
Bambance-bambancen binciken da aka yi bita shi ne I2 = 94.2% da nau'in bambance-bambance na Chi-squared = 310.06 (d.f = 18), P-value < 0.0001.
Nazarin ƙaramin-rukunin ya nuna cewa mafi girma na CƘB a tsakanin ma’aikatan jinya ya fito ne daga yankin Yammacin Afirka tare da yawan adadin kashi 68.46% (95% CI: 54.94-81.97; P-value < 0.0001) sannan yankin Arewacin Afirka ya biyo baya tare da yawan adadin kashi 67.95% (95% CI: 55.96–79.94; P-value < 0.0001).
Duk da cewa yawancin binciken da aka yi a halin yanzu yana ƙasa idan aka kwatanta shi da nazarin ƙasashen Yamma da Asiya, ya nuna cewa yawancin ciwon ƙasan baya a tsakanin ma’aikatan jinya yana da yawa.
Fiye da kashi 60% na ma’aikatan jinya na Afirka suna fama da ciwon ƙasan baya
Ma'aikatan jinya su ne mafi mahimmancin ma'aikatan sahun gaba a Afirka inda kayan kulawa da kiwon lafiya na iya yin ƙaranci.
Wannan binciken ya sake nazarin bincike masu daraja na shekaru 19 waɗanda suka nuna cewa fiye da kashi 60% na ma'aikatan jinya a Afirka suna fama da ciwon ƙasan baya (CƘB).
Ma’aikatan jinya suna da muhimmanci a Afirka, kuma yawan aiki yana yin tasiri a jikinsu.
A faɗin duniya, aikin jinya yana cikin manyan sana’o’i guda 10 a duniya idan ya zo ga haɗarin kamuwa da CƘB.
A gaskiyance ma, an bayar da rahoton cewa CƘB a cikin ma’aikatan jinya ya kai kashi 63% a Ostiraliya, kashi 56% a China, kuma har zuwa kashi 82.7% a wasu ƙasashen Afirka.
Masu bincike sun kalli wani nazari masu daraja na shekaru 19 don ganin yadda CƘB ya kasance a cikin ma’aikatan jinya a Afirka.
Sun bincika ta hanyar wallafe-wallafen kimiyya a cikin runmbunan bayanai daban-daban don nemo nazari daban-daban da aka buga tsakanin shekara ta 2000 zuwa ta 2018.
Masu binciken sun gudanar da wannan nazari mai tsari daga watan Satumba zuwa Nuwamba na shekarar 2018.
Binciken ya yi amfani da nazari guda 19 da suke da tarin ma’aikatan jinya 6110 daga yankuna daban-daban a duk faɗin Afirka.
Kashi 64.07% na ma’aikatan jinya a Afirka suna fama da ciwon ƙasan baya.
Binciken ya gano cewa Yammacin Afirka na da mafi yawan adadin ma’aikatan jinya da suke fama da CƘB da kashi 68.46%, sai Arewacin Afirka da ke biye da kashi 67.95%.
Masu binciken sun ce, kamar yadda suka sani, wannan binciken shi ne bita na farko da aka tsara da kuma nazarin ƙididdiga don bincika yadda CƘB ya yi ƙamari a cikin ma’aikatan jinya a Afirka.
Amma abin takaici, wasu yankuna a Afirka ba su da bayanan da aka samu, wanda zai iya sauya wasu sakamakon da aka ruwaito a cikin wannan binciken.
Kuma ko da yake alƙaluman da aka ruwaito a nan sun yi ƙasa sosai idan aka kwatanta su da na ƙasashen Yamma da na Asiya, waɗanda har yanzu suna da girma.
Masu binciken sun ba da shawarar cewa asibitoci da gwamnatoci a Afirka su samar da mafi kyawun yanayin aiki da dabarun rage damuwar aiki, da horar da ma’aikatan jinya wanda zai yi matuƙar rage haɗarin fuskantar CƘB.
Luganda translation of DOI: 10.1186/s12891-020-03341-y
Amharic translation of DOI: 10.1186/s12891-020-03341-y
Yoruba translation of DOI: 10.1186/s12891-020-03341-y
Northern Sotho(Sepedi) translation of DOI: 10.1186/s12891-020-03341-y