Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Masu Haɓaka Siten da Ƙarfin Aikin Etanol da kuma Halayen Fitar da Hayaƙi ta Amfani da Pyrorated Biodiesel

This is Hausa translation of DOI: 10.20944/preprints201806.0106.v1

Published onJul 23, 2023
Masu Haɓaka Siten da Ƙarfin Aikin Etanol da kuma Halayen Fitar da Hayaƙi ta Amfani da Pyrorated Biodiesel
·

Masu Haɓaka Siten da Ƙarfin Aikin Etanol da kuma Halayen Fitar da Hayaƙi ta Amfani da Pyrorated Biodiesel

Tsakure

A baya-bayan nan, buqatar nau’ukan mai masu arha, waxanda basa gurvata yanayi kuma masu wadatarwa ga buqatun al’umma na makashi ya qaru sosai.

Sinadarin etanol yana da karvuwa a matsayin hanyar samar da makamashi mai xorewa, gashi da yawan sinadarin oksijin.

Ana qirqirar etanol ne ta hanyar “etanolisis”.Sai dai a wannan binciken, an yi qoqarin haxakar dizel ne da man gurvataccen roba da etanol da kuma sinadari mai havaka mai, wato CI-0808 wanda aka siya daga kamfanin Innospec.

Babban dalilin haxa “siten” shi ne don qara qarfin tashin haxin zuwa xiqo 1 – 3.

Hanyonyin haxi guda biyar aka zava kamar haka:50:25:25, 60:20:20, 70:15:15,80:10:10 da 90:5:5 na Prolisis xin Man Gurvataccen Roba (wato Waste Plastic Pyrolysis Oil, WPPO), sai kuma etanol da man dizal (CD).

Wajen haxa sinadarin man kuwa, an zavi yawan kason da za a yi amfani da shi a matakin 0.01% na yawan man da aka haxa baki daxa.

A wannan aikin, WPPO da haxin dizal da sinarai masu inganta mai aka yi amfani da su a matsayin nau’in mai na daban.

An yi haka ne saboda gwada ingancin aikinsu da yanayin fidda hayakinsu a inji mai amfani da dizal mai tukunya xaya.

An haxa da CI-0808 saboda tsammanin zai iya rage fidda hayaqi na CO, UHC, NOX, PM da kuma qara lafiyar inji.

An gwada sakamakon binciken da aka samu da matakan ASTM kuma an yi bayani dalla-dalla ta hanyar amfani da zanen giraf da girge.

Abin da ya tabbata daga wannan binciken shi ne ana iya amfani da etanol da haxin WPPO a injinan dizal a matsayin mai ba tare da wasu sauye-sauye ba.

Indan aka yi amfani da haxin sinadari mai ingata mai wato ‘siten’ yana rage gurvataccen hayaqi sosai kuma yana qara ingancin inji daidai da man dizal da aka saba.

Summary Title

Mai da ake samu daga roba da mai da ake samowa daga qwayar halitta ka iya rage gurvataccen hayaqi na dizal

Masana sun rage gurvataccen hayaqi ta hanyar haxa mai da wasu sinadarai masu sabantuwa.

Haxin, wanda ya haxa da sinadarin etanol da mai wanda aka samo daga gurbataccen roba na da qarancin iskar da ke haddasa ciwon daji, kuma yana iya duk aikin da dizal yake yi.Dizal dai da aka saba da shi mai ne da ake samowa daga danyen man fetur, wanda yana xaya daga cikin abubuwan da ke haddasa sinarin xumamar yanayi.

Injinan dizal sun fi injinan gas qwari amma suna samar da sinadarin nitoro da sauran abubuwa masu haxari da kuma cutar da bil’Adama da gurvata yanayi.

Muradin wannan bincike shi ne gano hanyoyin samar da mai da sinadarai masu xorewa da za su taimaka wajen rage gurvataccen iska da ake samu daga dizal.

Binciken ya nuna a yi amfani da sinadarin etanol wanda ake samu dasu daga gurvataccen shara kamar itace da man girki da kuma mai da ake samu daga sabuntattun roba.

Waxannan dabaru ba su kai qwarin dizal ya kansu ba.Saboda haka, dole ne a qirqiro injina na musamman da za a yi amfani da su.Amma a wannan binciken za a yi amfani da su ne wajen rage gurvatacciyar iskar dizal da kuma amfani waxannan na’ukan mai a injinan dizal da aka saba da su.

Masu binciken sun haxa dizal da aka saba da shi (wato Conventional diesel, CD) da sinadarin etanol (wato E) da kuma mai da aka samo daga gurvataccen roba.

Sun kuma haxa da wasu sinadarai da ake siyarwa wandanda suke gyara sinadarin ‘siten’ wanda ake amfani da shi wajen gyara man dizal don ya rage fitar da guravataccen hayaqi.

Masu binciken sun yi amfani da injin dizal mai tukunya xaya a dakin bincike inda suka gwada aikin injinan ta hanyar amfani da nau’ukan man dabandaban.

Sun kuma gwada aikin injin wajen amfani da dizal kawai.

Masu binciken sun haxa sinadarin etanol da mai da aka samo daga gurvataccen roba da man dizal ta yanda za a iya rage gurvataccen hayaqi ba tare da an rage qwarin injin ba.

Haxakar 90% man dizal: 5% gurvataccen roba: 5% etanol wanda ke da mafi qarancin gurvataccen hayaqi kuma yana aiki daidai da man dizel da aka saba.

Sun kuma gano cewa amfani da hadakar man nan da kuma dizal ba ya kara zafin hayaki, wannan yana nufin ba ya rage lafiyar inji.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?