Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Yawan lalacewar hanta a tsakanin masu HIV da kuma abubuwa masu haɗari

Hausa translation of DOI: 10.1101/2020.11.16.384339

Published onAug 07, 2023
Yawan lalacewar hanta a tsakanin masu HIV da kuma abubuwa masu haɗari
·

Abubuwan da Suke Faruwa da kuma Haɗari na Haɗin Rigakafin Ciwon Hanta a Tsakanin Masu Fama da HIV a Asibitin Gundumar Bali ta Kamaru

Gabatarwa

Abun da yake faruwa na guba ga hanta abu ne mai barazana ga rayuwa kuma yana iya kawo cutar hanta ga masu amfani da magungunan jiyya na (cART) na tsawon lokaci.

Nazarinmu ya nemi kimanta abubuwan da suka faru da masu hasashen cART da suke haifar da cutar hanta (CIH) a tsakanin masu amfani da cART na tsawon lokaci a wani asibitin Gundumar karkara.

Hanyoyi

Wannan wani nazari mai zurfi ne na asibiti da aka yi a Asibitin Gundumar Bali.

An yi amfani da hanyar Spectrophotometric domin auna ma’aunin alanine-aminotransferase (ALT) da kuma matakan aspartate-aminotransferase (AST).

Marasa lafiya tare da haɓakar duka ALT da kuma AST an ɗauke su a matsayin CIH.

An yi amfani da gwajin murabba’in Chi (χ2), ANOVA da kuma nazarin ragi/ nazarin rayuwa na Kaplan Meier don tantance bayanan.

Sakamakon mutane 350 da suka shiga nazarin [156 (kashi 44.6%) maza da kuma mata194 (kashi 55.4%)], shekaru 43.87 ± 0.79 shekaru (zangon shekaru 20 – 84) sun shiga wannan nazari, 26 (kashi 4.4%) sun sami matsakaicin CIH.

Mun lura 57 (kashi 16.3%), 62 (kashi 17.7%) da kuma 238 (kashi 68%) matakan da suka ƙaru ALT + AST, ALT da kuma AST bi-da-bi.

Abubuwan tsinkaya masu zaman kansu guda biyu na CIH su ne, jinsi na maza da kuma shaye-shaye barasa yayin lokacin binciken.

Kammalawa

Yawaitar CIH a tsakanin marasa lafiya waɗanda suka kamu da HIV a Bali ya kasance ƙasa da wanda aka lura a binciken da suka gabata.

Tsawon lokacin jiyya ba shi da tasiri a kan yawan CIH.

Shaye-shayen barasa da kuma shan taba sun nuna bambance-bambance masu mahimmanci a cikin ci gaban CIH.


Yawan lalacewar hanta a tsakanin masu HIV da kuma abubuwa masu haɗari

Yawan lalacewar hanta a tsakanin masu HIV saboda haɗa magungunan MCƘ (Magungunan Cutar Ƙanjamau) ya ragu a asibitin gundumar Bali ta Kamaru, idan aka kwatanta da binciken da aka yi a baya.

Ko yaya, jinsi da shan barasa da kuma shan taba suna tasirin haɗarin lalacewar hanta ga masu HIV.

Yankin Afrika Kudu da Sahara na wakiltar fiye da rabin masu ɗauke da HIV a duniya.

Haɗin magungunan HIV shi ne magani da aka bayar da shawara, duk da haka tasirinsa yana haifar da lalacewar hanta a tsakanin marasa lafiya.

Yawancin bincike ba su mayar da hankali a kan lalacewar hanta da magungunan MCƘ suka haifar ba, don haka ana buƙatar ƙarin bayanai a kan wannan.

Masana kimiyyar sun so su gano adadin mutanen yankin da suke ɗauke da ƙwayar HIV tare da lalacewar hanta.

Sun kuma so su gano ko wane irin salon rayuwa ne yake ƙara haɗarin lalacewar hanta a tsakanin waɗannan marasa lafiya.

Masu binciken sun yi nazari a kan majinyatan asibitin gundumar Bali waɗanda suke ɗauke da ƙwayar HIV kuma ‘yan sama da shekaru 18.

An tattara samfuran jini daga duk marasa lafiya, kuma sun bincika ko akwai wasu furotoci da suke da alaƙa da lalacewar hanta ko a'a.

Daga nan sai suka yi amfani da samfurin kwamfuta domin tantance ko wane irin salon rayuwa ne yake da alaƙa da lalacewar hanta.

Masu binciken sun tabbatar da cewa matakan furotoci da suke nuna lalacewar hanta sun fi girma a cikin masu ɗauke da HIV.

Har ila yau, aikinsu ya nuna yadda wasu magungunan HIV suke da alaƙa da manyan matakan waɗannan furotoci.

Samfurinsu na kwamfuta ya nuna cewa maza masu shan magungunan MCƘ suna cikin haɗarin lalacewar hanta, da kuma mutanen da ke shan barasa da kuma taba.

TTuni an riga an san cewar masu ɗauke da HIV suna da haɗarin lalacewar hanta saboda magungunan da suke sha.

Duk da haka, wannan binciken ya yi la’akari da yadda masu HIV ke samun lalacewar hanta a asibitin gundumar Bali.

Haka nan masu binciken sun kuma gano cewa shan barasa da shan taba na sanya masu HIV cikin haɗarin lalacewar hanta.

Masu binciken sun yi gargaɗin cewa bayanan marasa lafiya na iya zama iyakancewa a wannan binciken.

Ba su yi la’akari da duk abubuwan ba, kamar amfani da wasu magunguna baya ga maganin HIV.

Har ila yau, tun da yawan jama’ar da aka yi amfani da su don wannan binciken ya bambanta da sauran nazarin ta fuskar shekaru da kuma jinsi, ba lallai ne sakamakon ya zamo ɗaya da sauran nazari daga Afirka ba.

Wannan binciken ya mayar da hankali ne ga wani asibiti a ƙasar Kamaru kuma ya kamata a tabbatar da sakamakon binciken a bincike na gaba a wasu yankuna.

Afirka tana da babbar matsalar HIV.

Wannan binciken daga masu bincike na ƙasar Kamaru ya yi ƙarin haske kan muhimman bayanai da ke nuna yadda masu HIV ke fama da lalacewar hanta, kuma abubuwa daban-daban na ƙara illa ga lalacewar hanta.

Samun wannan bayanin na iya taimakawa wajen kula da lalacewar hanta a tsakanin masu HIV.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?