Description
This is a lay summary of the article published under the DOI: 10.1038/s41598-021-96330-7
Hausa translation of DOI: 10.1038/s41598-021-96330-7
Shanun Sudan na asali, wato Baggara na naman sa da Butana da Kenana na kiwo, suna da halaye masu daidaituwa da kuzarin aiki a yanayin noma a cikin zafi da bushewar ƙasa.
Don haka, su ne makiyaya da makiyaya masu yawo suka fi amfani da su.
Mun yi nazarin bambance-bambance da tsarin ƙwayoyin halitta na BoLA-DRB3, wani wuri na ƙwayoyin halitta da ke da alaƙa da amsawar garkuwar jiki ga shanun asali na Sudan da kuma a cikin mahallin ma’ajiyar shanu ta duniya.
Samfurin jini (n = 225) aka ɗauka daga nau’o’in asali guda uku (Baggara; n = 113, Butana; n = 60 da Kenana; n = 52) da aka rarraba a yankuna shida na ƙasar Sudan.
An ƙirƙira jerin abubuwan nukiliyatayid ta hanyar yin amfani da hanyar buga jerin abubuwan.
Mun bayyana aliyas 53, ciki har da sababbin aliyas guda bakwai.
Binciken babban ɓangaren (PCA) na jakunkuna furotin da ke cikin aikin ɗaurin-antigen na rukunin MHC ya nuna cewa jakunkuna 4 da 9 (bi da bi) sun bambanta nau'in Kenana-Baggara da Kenana-Butana daga sauran nau’o’in.
Binciken Venn a kan nau’o’in shanu na Sudan, Kudu-maso-Gabashin Asiya da Turai da kuma Amurka tare da aliyas 115 ya nuna 14 sun bambanta da nau’o’in Sudan.
Rarraba mitar ƙwayoyin halitta na shanun Baggara ya nuna rabe-raben madaidaicin zaɓi, yayin da fihirisar zaɓi (ω) ya bayyana kasancewar zaɓi mabambanta a rukunin amino acid da yawa tare da BoLA-DRB3 exon 2 na waɗannan nau’o’in na asali.
Sakamakon PCA da yawa sun yi daidai da tsarin tari da aka gani a kan bishiyoyin haɗin-gwiwa (BH).
Waɗannan sakamakon sun ba da haske game da yawan tsirarsu ga kamuwa da cututtuka daban-daban na wurare masu zafi da ƙarfin haihuwa a cikin yanayi mara kyau na Sudan.
Masana kimiyya sun gano wasu nau’o’in ƙwayoyin halitta na musamman a cikin shahararrun nau’o’in shanun Sudan da ake ganin suna sa su zama masu juriya ga kamuwa da cututtuka, kuma binciken zai iya haifar da ingantattun dabarun kiwo.
Bambance-bambance a cikin ƙwayoyin halitta, da ake kira aliyas, galibi suna haifar da halaye na musamman kamar taurin da ake gani a cikin ɗaiɗaikun dabbobi ko tsirrai.
Nau’o’in shanu guda uku, Baggara da Butana da kuma Kenana, sun shahara wajen juriya, kuma makiyayan da ke faɗin ƙasar Sudan ke ajiye su domin samun nama da madara.
Bincike a kan nau’o’in shanu a wajen Afirka sun nuna cewa nau’o’in aliyas na ƙwayoyin halitta da ake kira BoLA-DRB3, wanda ke taka rawa a cikin tsarin garkuwar jiki, na iya sa dabbobin su jure wa kamuwa da cututtuka ko ƙwari.
Amma har ya zuwa yanzu, masana kimiyya kaɗan suka sani game da bambancin wannan ƙwayar halitta a cikin nau’o’in shanu na Afirka.
A wannan binciken, masu bincike sun bincika BoLA-DRB3 a shanun Sudan don gano ko da dabbobin suna da wani aliyas na musmaman wanda zai iya bayyana juriyarsu ta kamuwa da cuta da kuma ba da haske ga waɗannan nau’o’in don nazarin gaba.
Masu binciken sun tattara jini daga dabbobi 225 a faɗin ƙasar Sudan.
Daga nan sai suka gudanar da nazarin ƙwayoyin halitta na samfurorin, don gwajin bambance-bambance a cikin ƙwayoyin halittar BoLA-DRB3.
Daga nan sai suka kwatanta abubuwan da suka gano da bayanan da ake da su game da ƙwayar halittar da ke cikin wasu shanu.
Haka kuma sun kuma duba sau nawa nau’o’in aliyas suka bayyana a cikin samfuransu, don gwadawa da gano dalilin da yasa kowane irin sauye-sauye za su iya faruwa.
Gabaɗaya, shanun Sudan suna da nau'o’in ƙwayoyin halittar BoLA-DRB3 masu yawa da masu binciken ke tunanin za su iya inganta garkuwar jikinsu kuma ya sa su zama masu juriya ga kamuwa da cututtuka.
Masu binciken sun gano aliyas guda bakwai waɗanda sababbi ne kuma na musamman ga nau’o’i na Sudan.
Sun kuma gano cewa, idan aka kwatanta da shanu daga wasu sassa na duniya, samfuransu sun haɗa da aliyas 14 na ƙwayoyin halittar BoLA-DRB3 waɗanda dabbobin da ba na Afirka ba, ba su da su.
Waɗannan halaye na musamman na iya taimakawa shanun Sudan su tsira daga haɗuwar cututtuka da matsalolin jiki, kamar zafi, wanda yake gama-gari a muhallinsu.
Binciken ya ba da sakamako na farko mai zurfi game da bambancin ƙwayoyin halitta a cikin ƙwayar halittar BoLA-DRB3 a cikin shanun Afirka.
Sababbin aliyas ɗin da aka gano sun kuma buɗe ƙofa ga bincike na nan gaba game da juriyar kamuwa da cututtuka a cikin shanu, da kuma yadda za a iya inganta shirye-shiryen kiwo.
Wani muhimmin batu don bincike na gaba shi ne ainihin rawar da sababbin aliyas ɗin ke takawa a cikin amsar garkuwar jikin shanun.
A yayin da wasu sauye-sauye suke ƙara juriyar kamuwa da cututtuka, wasu na iya sa dabbobi saurin kamuwa da wasu cututtuka.
Don haka, nazari na gaba zai buƙaci bincika dangantakar da ke tsakanin aliyas daban-daban da kuma cututtukan shanu.
A matsayinsa na farko a Afirka, binciken wani muhimmin ci gaba ne ga bincike a kan ƙwayar halittar BoLA-DRB3 da kuma aikin garkuwar jiki.
Masana kimiyya daga Sudan da Lebanon da Saudi Arabia da Japan da Argentina sun yi aiki tare a kan wannan aikin.
Northern Sotho(Sepedi) translation of DOI: 10.1038/s41598-021-96330-7
Amharic translation of DOI: 10.1038/s41598-021-96330-7
Yoruba translation of DOI: 10.1038/s41598-021-96330-7