Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Baƙin jinsuna na yin barazana ga ɗimbin halittu a Afirka ta Kudu

Hausa translation of DOI: 10.1007/978-3-030-32394-3_17

Published onMay 19, 2023
Baƙin jinsuna na yin barazana ga ɗimbin halittu a Afirka ta Kudu
·

Ƙimar Tasirin Tasirin Baƙin Jinsuna a kan Ɗimbin Halittu a Afirka ta Kudu ta Amfani da Hanyoyi Daban-daban

Tsakure

 A yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike a kan tasirin baƙin jinsuna a kan muhalli, kuma ana ci gaba da yin muhawara kan yadda za a daidaita bayanin waɗannan tasirorin.

Wannan babin ya kimanta yanayin ilimi kan tasirin baƙin jinsuna a kan ɗimbin halittu a ƙasar Afirka ta Kudu bisa hanyoyin tantancewa mabambanta.

Duk da cewa ƙasar Afirka ta Kudu tana ɗaya daga cikin ƙasashe masu bambance-bambancen ɗimbin halittu a duniya, an sami 'yan bincike kaɗan da suka tattara bayanan tasirin baƙin jinsuna a kan ɗimbin halittu.

Mafi yawancin abin da aka sani ya dogara ne a kan ra'ayin masana, kuma saboda haka matakin amincewa da ƙididdiga na girman waɗannan tasirin ya yi ƙaranci.

Duk da haka, a bayyane yake cewa yawancin baƙin jinsuna suna haifar da mummunan tasiri, kuma cewa akwai dalili na sa damuwa mai tsanani.

An sami haɓaka wajen ƙoƙarin duniya don tantance dukkan baƙin jinsuna tare da daidaitattun ka’idoji don rage matsalar kwatanta tasirin da aka auna ta amfani da hanyoyi mabambanta.

An gudanar da kƙima na yau da kullum ga wasu baƙin jinsuna kaɗan a ƙasar Afirka ta Kudu, amma ba a tantance yawancin jinsuna da suka zama ‘yan gida da kuma masu cin zarafi ba, kuma, muna zargin, babu wani yunƙuri na tantance galibin baƙin jinsuna da kuma tasirinsu.

Duk da haka, tsarin jan-jeri sun gano cewa ana haɗa baƙin jinsuna akai-akai a zaman babban haɗarin ƙarewa ga jinsunan kifaye na gida da yawa da dangogin dabbobi masu buƙatar ruwa ko danshi don rayuwa da kuma shuke-shuke da yawa.

Akwai bincike kaɗan da suka tattara haɗin gwiwar sake aukuwar tasirin baƙin jinsuna da ke faruwa a wasu yankuna na musamman, kuma waɗannan bincike suna iya bayar da hujjoji na kulawa da kuma gudanarwa, wanda galibi akan rasa.

A yayin raguwa saboda baƙin jinsuna wajen ƙimar sabis na yanayin muhalli na gida, yawan amfanin gona da rashin lafiyar ɗimbin halittu suna da ƙaranci a halin yanzu, ana sa ran waɗannan tasirin za su girma cikin sauri yayin da wasu jinsuna masu ɓarna suka shiga wani mataki na girma.


Baƙin jinsuna na yin barazana ga ɗimbin halittu a Afirka ta Kudu

Masu bincike sun kwatanta binciken da aka gudanar don gano baƙin jinsuna da suke yin barazana ga ɗimbin halittu na Afirka ta Kudu.

 Ƙasar Afirka ta Kudu tana ɗaya daga cikin yankuna masu ɗimbin tsirrai a duniya.

Aƙalla baƙin jinsuna guda 107, kashi 75% na tsire-tsire ne, ana zargin suna da munanan tasiri manya a kan ɗimbin halittun ƙasar.

Ba a san waɗannan tasiri da ake zargin waɗannan jinsuna suke da su ba saboda ƙarancin nazarin da zai iya yarda game da mene ne ainihin waɗannan illoli.

 Baƙin jinsuna suna iya rage ɗimbin halittu ta hanyoyi mabambanta.

An san hanya ɗaya a matsayin haɗaɗɗiya, inda suke gauraya ta asali tare da jinsunan gida.

Haka nan baƙin jinsuna kuma na iya farautar nau’in 'yan ƙasa zuwa ga ɓacewa.

Haka nan baƙin jinsuna na iya kawo sababbin cututtuka kuma suna haifar da lalacewar muhalli, kamar bishiyoyin da suke amfani da ruwan ƙasa da yawa.

Wannan binciken ya tattara duk bayanan da ake da su game da tasirin baƙin jinsuna a kan ɗimbin halittu a Afirka ta Kudu.

 Masu binciken sun duba yadda takamaiman jinsunan baƙi suka canza yanayin muhallin gida da kuma irin jinsuna 'yan asalin da suke yi wa barazana.

Sun sake bitar nazarin da suka yi amfani da daidaitattun makin tasiri, kuma sun yi magana da masana don jin ra'ayoyinsu.

Har ila yau, sun duba jinsunan gida da a halin yanzu suke cikin haɗarin ɓacewa kuma sun yi amfani da waɗannan "jajayen jerin" don ganin ko baƙin jinsunan don suna da hannu a raguwarsu.

Binciken ya gano cewa yawancin jinsunan dodon koɗi da kifi da dabbobi masu shayarwa, da tsirrai suna da hannu wajen barazana ga jinsunan asali.

 Alal misali, dodon koɗi mai gurzunu-gurzunu yana ɗaya daga cikin jinsunan dodon koɗi guda huɗu masu mamayewa a ƙasar Afirka ta Kudu.

Ya mamaye koguna da tafkuna da ciyayi da dama a gabashi da arewacin ƙasar, inda ya mamaye jinsunan dodon koɗi na gida.

 Kifi mai Ƙaton Baki yana ɗaya daga cikin jinsunan kifaye guda biyar masu mamayewa a Afirka ta Kudu da aka sani da sanannun tasiri.

Ya rage jinsunan kifi na asali zuwa ga gushewa a cikin ruwa na Afirka ta Kudu da dama.

Dangane da dabbobi masu shayarwa, binciken ya gano cewa Baƙin Ɓera (Rattus rattus) yana ɗaya daga cikin jinsunan baƙin dangin ɓeraye masu cin zarafi da suka yi sanadiyyar ɓacewar wasu tsuntsaye da ƙwari da kuma jemagu da sauran dangin ɓeraye ta hanyar farautarsu da cin abincinsu ko yaɗa cututtuka.

Ko da yake tasirin waɗannan baƙin jinsuna a kan ɗimbin halittu har yanzu yana da ɗan ƙaranci, masu bincike suna tsammanin mummunan tasirin su zai yi munana sosai idan ƙasar Afirka ta Kudu ba ta dakatar da haɓakarsu ba.

Wannan binciken shi ne matakin farko na daidaita yadda za a iya auna tasirin baƙin jinsunan a ƙasar Afirka ta Kudu.

 A yayin da binciken ya iya tantance adadin ɓarnar da baƙin da suka mamaye ƙasar Afirka ta Kudu suka yi, ya kasa ƙididdige ɓarnar da aka yi a inda fiye da baƙin jinsuna ɗaya suke wanzuwa a cikin wani yanayin muhalli na gida.

Ba tare da irin wannan bincike ba, gwamnatoci da sauran hukumomin da ke kula da su ba za su sami bayanan da za su kare ɗimbin halittu na gida ba.

A yanzu, masu binciken sun shawarta cewa dokoki a ƙasar Afirka ta Kudu kamata ya yi su mayar da hankali wajen bayar da fifiko a kan baƙin jinsuna da aka jero a cikin wannan takarda don taƙaita lalacewar ɗimbin halittu na gida.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?