Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Wata Hanyar Tsaro mai Gano Muhimman Masu Kulawa da Cutar Kansar Mahaifa na mai HPV

This is Hausa translation of DOI: 10.1101/2020.05.12.20099424

Published onJul 23, 2023
Wata Hanyar Tsaro mai Gano Muhimman Masu Kulawa da Cutar Kansar Mahaifa na mai HPV
·

Wata Hanyar Tsaro mai Gano Muhimman Masu Kulawa da Cutar Kansar Mahaifa na mai HPV

Tsakure

Ciwon dajin mahaifa shi ne wanda ya fi yawa da kisan mata a duniya.Ya kasha sama da mata 250,000 a shekarar 2019.

Kusan kashi casa’in da biyar na ciwon dajin mahaifa na da alaqa da qwayar cuta mai qarfi da ke mamaye Tsarin halittan Xan’Adama da aka fi sani da Human Papillomavirus (HPV) kuma da kashi saba’in cikin waxannan na da alaqa da haxakar qwayoyin cuta a cikin qwayar halittan da suke ciki.

Qwayar cutar HPV tana sa sauye-sauye cikin tsarin daidaito qwayar halittar da ta kamu da ciwon daji wanda za a iya ganowa ko magancewa.

Anan, mun yi amfani da tsare-tsaren bincike a kan wannan tsarin chanje-chanje da kuma tsarin sinadarin protin da suke da alaqa da shi, wanda aka samo daga masu cutar ciwon dajin mahaifa masu ciwon HPV.

Mun yi amfani da gwajin hanyoyi don nuna cewar ciwon dajin da ke da nasaba da HPV na da kawcewar hanyoyin qwayar halitta da dama, musamman ma waxan da ke haxe da gurbi qwaya, mitosis, sitokin da qyaryar kariya.

Mun yi amfani da hangen lissafi wajen nuna cewa ciwon daji mai alaqa da cutar HPV ya dogara da abubuwa da yawa kamar SOX2, E2F, NANOG, OCT4 da MYC waxanda ke rike da abubuwa da yawa kamar sabunta qwayar halitta mai ciwon daji da kuma yaxawa da bambanta qwayar ciwon daji.

Ta hanyar lura da abin da ke faruwa cikin mahaxar qwayar halitta da ake kiran kinasis, mun fitar da qwayoyin protin masu alaqa da kinasis kamar MAPK1, MAPK3 da MAPK8 da kuma kinasis mai dogaro da siklin kamar su CDK1, CDK2 da CDK4 wanda shi ne kinasis mafi qarfi da ke juya jikin qwayar ciwon dajin mahaifa mai alaqa da HPV.

Duka-duka dai, mun gano hanyoyin daidaito da sinadaran protin dake da alaqa da ciwon HPV mai haddasa ciwon dajin mahaifa.Wannan zai taimaka wajen samo magunguna masu amfani wajen jinya nan gaba.

Summary Title

An samo magani dake iya warkar da ciwon daji mai alaqa da HPV

Summary Body Text

Masu bincike sun gano wasu qwayoyin halitta na musamman da hanyoyi waxanda za a iya amfani da su wajen warkar da mata masu ciwon daji na mahaifa wanda ke da alaqa da Tsarin halittan Xan’Adama da aka fi sani da Human Papillomavirus (HPV).

Sun dogara da bayanai da aka samo daga marasa lafiya da kuma fahimtar hasashen lissafin wajen ambaton cewa za a iya dogaro da wasu yanaye-yanayen sauyi da qwayoyin protin waxanda ke daidaita girma da rarrabuwar qwayoyin halitta baixaya wajen magance ciwon daji ta hanyar terafi.

Kusan kashi 90% na ciwon dajin mahaifa na faruwa ne a qasashe masu tasowa waxanda ba su qarfin kula da lafiya.

Wannan ciwon ya fi kowane ciwon daji hatsari ga mata, kuma yana kisan mata sama da 300 000 a shekara a faxin duniya.

Kafin gudanar da wannan binciken, ma’aikatar ilimin ciwon daji da ake kira da Cancer Genome Atlas Project da sauransu sun fito da qwayoyin halitta da sinadaran protin da ake samu a ciwon dajin mahaifa.

Matsayin qwayoyin halitta, masan sun kawo zantuka a kan bambamcin yanayin lafiyaiyar mahaifa da kuma wacce take dauke da ciwon daji.

Manufar wannan binciken shi ne gano yanda wannan bambamcin ke tasowa; ko ma mu ce, yanda sinadaran protin da qwayoyin halitta da suke cikin ciwon dajin mahaifa ke wanzuwa, raguwa, tashi ko sauka.

Ta hanyar gano manyan qwayoyin halitta da ke cikin tsarin sauyin halitta ko sinadaran protin, masu bincike kan iya samar da magunguna da za su iya toshe hanyoyi musamman da qwayoyin ke canjuwa.

Don gano tsarin waxannan qwayoyin halitta da hanyoyinsu, masu bincike a Zambiya da Afirka ta Kudu sun kwatanta bayanan gwayar halitta daga masu ciwon dajin mahaifa da ke da cutar HPV, da waxanda ba su da cutar HPV da kuma bayanai daga marasa lafiyan da ba su da ciwon dajin mahaifa.

Da zarar sun gano bambamcin da ke da akwai cikin marasa lafiya masu HPV sai su yi amfani da wata na’ura mai qarfi don su haqaito hanyoyin daidaiton da waxancan qwayoyin halitta ke amfani da su.

Babbam abin da suka gano shi ne HPV na shafar hanyoyin girma da rarrabuwar qwayoyin halitta.Saboda haka marubutan suka ba da shawarar cewa ana iya magance ciwon dajin mahaifa ta hanyar magungunan da za su hari waxannan hanyoyin.

Wannan ya yi daidai da sakamakon binciken ilimin lafiya da suka gabata cewa ciwon dajin mahaifa na jin maganin da ke kama yanayin qwayoyin halitta.

Haka kuma binciken ya yi manuniya ga hanyoyi da ke da nasaba da kumburi da kariya.

Masu binciken sun ce ana buqatar qarin bincike don gano bambamcin da ke tsakanin hanyoyin qwayar halitta dake haddasa nau’ukan ciwon daji dabam-dabam.

Tunda kashi 95% na cutar ciwon dajin mahaifa na da alaqa da qwayoyin cuta masu xauke da HPV, gano yanda cutar ke mu’amala da qwayoyin halitta a jikin xan’adam na da muhimmanci wajen samar da jinya ga mata a Afirka da ma duniya baki xaya.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?