Description
This is a lay summary of the article published under the DOI: 10.1007/978-3-319-93438-9_1
Hausa translation of DOI: 10.1007/978-3-319-93438-9_1
Zaɓin nau’in mai tara hasken rana don aiki da adadin zaɓaɓɓun masu tarawa don amfani daga baya, tsari ne na yanke shawara mai muhimmanci, wanda zai iya yin tasiri sosai ga sha'awar tattalin arziƙin tsarin ɗumama ruwa da hasken rana.
A cikin wannan takarda, an samar da samfurin tattalin-zafi don ƙididdige ma’auni mai dacewa wanda zai iya taimakawa wajen zaɓar mafi kyawun mai tarawa don amfani da shi a cikin tsarin ɗumama ruwa da hasken rana da kuma ƙayyade ma’auni mafi kyau na girman kayan aikin na’urar ɗumama ruwa da hasken rana da zarar an zaɓi mai tattarawar.
Ma’aunin kwatanta makamashi-ga-kowace-dala, wanda aka ƙididdige shi a zaman fitarwar makamashin zafi na shekara-shekara na mai tarawa a cikin matsakaiciyar shekara, a abin da ake kira girman “wuri-mai-kyau” girman tsararrun mai tarawa, wanda aka raba ta hanyar kuɗin sake zagayowar rayuwa na shekara-shekara, bisa la’akari a kan rayuwar garanti da farashin farko na mai tarawa, an ba da shawarar a matsayin koyarwa don kwatanta ingancin farashi na masu tara hasken rana daban-daban.
Don ƙayyade girman wuri-mai-kyau na mai tarawa don amfani da shi a cikin wani tsarin ɗumama ruwa da hasken rana, inda ake ƙididdige adadin makamashi-ga-kowace-dala, An yi amfani da Tabbataccen Ƙimar Rana na Yanzu a matsayin aikin haƙiƙa don haɓaka.
Nau’o’i goma (10) daban-daban na masu tara zafin rana na ruwa (lebur guda 5 da nau’i masu bututu guda 5), waɗanda aka kimanta ta Solar Ratings & Certification Corporation (SRCC), an jera su bisa ga ma’aunin makamashi-ga-kowace-dala ta hanyar samfurin tattalin-zafi da aka bayyana a cikin wannan binciken.
A wuri mai kyau na mai tarawa na na’urar ɗumama ruwa da hasken rana, madaidaicin adadin tankin ajiyar ruwan zafi da mafi kyawun adadin hasken rana shi ma lokaci guda ana ƙayyadewa.
Adadin ma’ajiyar ruwan zafi da ake buƙata yana raguwa yayin da yankin mai tarawa ya ƙaru yayin da adadin hasken rana ya ƙaru, tare da raguwar haɓakar rataye, har sai ya cika da ƙimar haɗin kai.
Don wannan nazari na yanzu inda yanayin zafin da ake buƙata shi ne 50 ° C kuma na’urar ɗumama ruwa na hasken rana yana tsakiyar ƙasar Zimbabwe (layin da ya zagaye duniya 19 ° K da layin da ya keta duniya 30 ° G), samfurin mai tarawa da aka zaɓa ya kasance nau’in-lebur, wanda ya sami maki mafi girma na makamashi-ga-kowace-dala na 26.1 kWh/$.
Mafi girman wannan samfurin mai tarawa don ƙaddamarwa a cikin na’urar ɗumama ruwa na hasken rana a wurin nazarin binciken shi ne 18 m2 a kowace m3 na buƙatar ruwan zafi na yau da kullum; tare da adadin ajiyar ruwa mai zafi na 900 l/m3; a mafi kyawun adadin hasken rana na 91%.
Ko da yake hanyar wannan takarda an yi amfani da ita ne kawai don aikace-aikacen ɗumama ruwa da hasken rana na ƙayyadaddun yanayin sarrafawa, a ƙayyadajjen wuri, ana iya amfani da shi daidai da kowane aikace-aikacen ɗumama ruwa da hasken rana a kuma kowane wuri.
A yayin da ƙasar Zimbabwe take fama da buƙatar wutar lantarki, gwamnatin ƙasar ta ba da shawarar yin amfani da na'urorin ɗumama ruwa da hasken rana wajen daidaita buƙatun wutar lantarki.
Wannan binciken ya gano tsarin ɗumama ruwa da hasken rana mafi arha wanda ya fi dacewa da ƙasar Zimbabwe, ta hanyar amfani da samfurin da za a iya amfani da shi ga kowace ƙasa.
Na'urar ɗumama ruwa da hasken rana na amfani da hasken rana don ɗumama ruwa don amfanin gida, kuma a ƙasar Zimbabwe, wannan tsarin na zama wani zaɓi mai ƙayatarwa a yayin da ƙasar take fuskantar cunkoso.
Duk da haka, waɗannan na’uorin na iya zama masu tsada da nau'o'i daban-daban kuma samfurori daban-daban suna da fasaloli da girma mabambanta, kuma suna da damammaki daban-daban wajen ɗumama ruwa yadda ya kamata.
Masu binciken sun yi amfani da samfurin lissafi don nemo madaidaicin girman nau'in kayan tattarawa na tsarin ɗumamawa wanda zai samar da zafi mai yawa daga rana a mafi ƙarancin farashi.
Don nemo wannan "wuri mai kyau" masu binciken sun tantance makamashin zafin da kowane tsarin zai tattara daga rana har tsawon shekara guda, kuma sun raba shi da farashinsa cikin daloli don nemo ma'aunin makamashi-ga-kowace-dala.
Binciken ya yi amfani da samfurin Tabbataccen Ƙimar Rana na Yanzu don samfuran na’uorin ɗumama ruwa da rana guda 10 kuma ya sanya su daga mafi girman makamashi-ga-kowace-dala zuwa mafi ƙaranci.
Masu binciken sun kuma yi amfani da yawa, ko adadin ruwan da kowace na’ura za ta iya ɗumamawa don ƙayyade ma'aunin makamashi-ga-kowace-dala.
Saboda wannan shi ne mafi girman mai tara zafin rana, ƙarancin ruwan zafi da na’urar za ta iya ƙunsa, kuma wannan binciken ya yi nufin gano "wuri mai kyau" tsakanin yawan ruwan zafi da girman mai tarawar ma.
Binciken ya gwada na'urorin ɗumama ruwa da hasken rana guda 10 a 50 C, yanayin zafin da ake yi a tsakiyar ƙasar Zimbabwe yana layin da ya zagaye duniya 19° ta Kudu da layin da ya keta duniya 30° ta Gabas.
Haka nan masu binciken sun gano cewa mafi kyawun zaɓi, kuma mafi arhar zaɓin ɗumama ruwa da zafin rana shi ne mai tara nau'in-lebur wanda ke da mafi girman ƙimar makamashi-ga-kowace-dala na sa'o'i 26.1 kiloWatt ga kowace dala (kWh/$).
Da wannan takamaiman samfurin na’urar ɗumama ruwa da hasken rana, masu binciken sun yi ƙiyasin cewa zai iya ɗumama ruwa lita 900 ta hanyar amfani da kashi 91% na iska mai guba ta rana da yake samu daga rana.
Waɗannan sakamako sun shafi na'urorin ɗumama ruwa mai amfani da hasken rana a ƙasar Zimbabwe, amma masu binciken sun ba da shawarar cewa za a iya amfani da samfurin da suka yi amfani da shi a cikin wannan binciken ga kowane tsarin ɗumama ruwa da hasken rana a kowane wuri.
Amharic translation of DOI: 10.1007/978-3-319-93438-9_1
Luganda translation of DOI: 10.1007/978-3-319-93438-9_1
Yoruba translation of DOI: 10.1007/978-3-319-93438-9_1
Northern Sotho translation of DOI: 10.1007/978-3-319-93438-9_1