Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Yawaitar Mutuwar Mazakuta cikin Marasa Lafiya masu Ciwon Suga da Alaqarsa da Nauyin Jiki da Sinadarai masu Alaqa da Suga a Afirka

This is Hausa translation of DOI:10.1155/2020/5148370

Published onJul 24, 2023
Yawaitar Mutuwar Mazakuta cikin Marasa Lafiya masu Ciwon Suga da Alaqarsa da Nauyin Jiki da Sinadarai masu Alaqa da Suga a Afirka
·

Yawaitar Mutuwar Mazakuta cikin Marasa Lafiya masu Ciwon Suga da Alaqarsa da Nauyin Jiki da Sinadarai masu Alaqa da Suga a Afirka

Tsarerren Waiwayen Aiyuka da suka Gabata

Tsakure

ShimfiƊda.

Mace-mace da tsananin ciwo cikin masu ciwon suga na da alaqa da qanana da manyan matsaloli da suka shafi zuciya.

Saidai, akwai bambamci mai yawa cikin binciken da aka gudanar kan DM wajen yawaitar mutuwar azzakari a Afirka.

Saboda haka, wannan binciken na nufin qiyasta yawaitar masu ED da DM da alaqarsa da nauyin jiki (BMI) da sinadarin protin mai tafiyar da numfashi a Afirka.

Hanyoyi.

An binciko matattarar aiyuka na PubMed, Web of Science, Cochrane Library, Scopus, PsycINFO, African Journals Online, and Google Scholar don tsamo binciken da aka yi kan ED ckin masu ciwon DM.

An yi amfani da tsarin funel plot da tsarin baibai na Egger don son rai ke cikin ko wani bincike.

An yi amfani da lissafin I2 don gano bambamce-bambamce da ke tsakanin aiyukan da su ka gabata.

An yi amfani da tsarin DerSimonian da taswirar gano tasiri na Laird don awna yawan tasirin faxin aiyukan.

An awna bayanan ta hanyar kwatanta su bisa qasa, yawan mutanen da aka yi bincike a kansu, da shekarar wallafa aiki.

An yi amfa da nazarin fahimtar alaqa don gano tasirin xaya daga cikin aiyukan kan lissafin da aka samu baki xaya.

An yi amfani da taswirar lissafi na STATA na 14 wajen gudanar da nazarin.

Sakamako.

Binciken ya dubi aiyuka 13 da aka yi kan mutane 3,501.

Mun yi hasashen cewa yawaitar ED cikin masu DM a Afirka da kai mizanin kashi 71.45% (95% CI: 60.22–82.69).

Masu ciwon suga da suke da mizanin nauyin jiki na ≥30 kg/m2 sunfi kamuwa da ED da wajen kashi 1.26 wato (AOR = 1.26; 95% CI: 0.73–2.16) waxanda sinadari mai tafiyar da numfashi ya nuna maki <7% na da qarancin kamuwa da ED (AOR = 0.93; 95% CI: 0.5–5.9) da kashi 7%, ko da yake masu da cikakkar alaqa da ED.

Kammalawa.

Yawaitar ED cikin masu DM a Afirka na da yawa.

Saboda haka, a aiwatar da matakai daidai da yanayi da kariyar da ta dace da kevavvun yanayin ko wane qasa don rage yawaitar ED cikin marasa lafiya masu fama da DM.

Summary Title

Kasha 70% cikin maza masu ciwon suga sun ce suna fama da mutuwar azzakari

Miliyoyin mutane a faxin duniya masu ciwon suga na fama da mutuwar azzakari, amma ba a san adadin ba a Afirka kawo yanzu.

A shekarar 2017, kusan mutane miliyan 425 suke fama da ciwon suga (DM) a faxin duniya, kuma ana hasashen qaruwar wannan adadin zuwa miliyan 629 a shekarar 2045.

Mutuwar azzakari na xaya daga cikin illolin ciwon suga da ba a lura da su, wanda shi ne rashin qarfin azzakari da zai iya wadatar da jima’i.

A samu mutuwar azzakari a kashi 49% cikin maza masu ciwon suga a Ingila, 35.8% a Italiya, 77.1% a Afirka ta Kudu, da 67.9% a Gana.

Sai dai bayanai daga Afirka sun bambanta sosai, saboda haka masu bincike sun kwatanta bayanan don su gano yanda mutuwar azzakari yake cikin masu ciwon suga, kuma a gano alaqarsa da nauyin jiki da yawan sugar jini.

Masu binciken sun binciko cikin laburaren PubMed, Web of Science, Laburaren Cochrane, Scopus, PsycINFO, African Journals Online, da Google Scholar don tsamo binciken da aka yi kan mutuwar azzakari cikin masu ciwon suga.

Sun yi amfani da hanyoyin lissafi masu yawa wajen nazarin sakamon binciken guda 13 da aka yi kan mutane 3,501.

Sun yi awon daidaito tsakanin aiyukan don tabbatar da cewa babu aiki guda xaya da ya rinjayi saura, wanda hakan zai iya kawar da lissafin yawaitar mutuwar azzakari cikin mutanen da aka yi bincike a kansu.

Binciken ya gano akwai mutuwar azzakari cikin kashi 71.45% na maza masu ciwon suga a Afirka.

Sun gano cewar masu ciwon suga da suke da nauyin jiki wanda ya wuce mizani sun fi kamuwa da mutuwar azzakari da xigo 1.26.

Sun kuma gano cewar masu ciwon suga waxanda suke da daidaiton sugar jini, wanda ake ganowa in sinadarin protin mai tafiyar da numfashi cikin jini ya tsaya a kashi 7%, na da qarancin samun mutuwar azzakari da kashi 7%.

Binciken na da illoli waxanda ya kamata a duba cikin bincike nan gaba.

Na farko, ya na da wuya a gano ko sakamakon binciken da aka yi a mabambanta qasashe na iya wakiltar nahiyar baki xaya, domin babu bayanai da aka samu kan nahiyar Afirka baki xaya.

Na biyu, binciken ya dogare ne kan muqalun da aka yi cikin harshen Ingilishi kaxai, wanda hankan na nufin binciken ka iya barin bayanai masu amfani sosai da aka wallafa cikin wasu harsuna.

Wannan sakamon ya nuna cewar a akwai yawaitar mutuwar azzakari cikin masu ciwon suga a Afirka.

Masu binciken sun ba da shawarar xaukan matakai daidai da kevavvun yanayin ko wane qasa.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?