Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Kwaikwaya da Inganta Tsarin Wutar Lantarki na Makamashi mai Sabantuwa ga Semonkong, Lesotho

This is Hausa translation of DOI: https://doi.org/10.1007/978-3-319-93438-9_9

Published onJul 22, 2023
Kwaikwaya da Inganta Tsarin Wutar Lantarki na Makamashi mai Sabantuwa ga Semonkong, Lesotho
·

Tsakure

Duwatsu masu kauri da tsaunuka tare da ƙauyukan karkara marasa yawan jama'a sun nuna mafi yawan yanayin ƙasar Lesotho, wanda ya sa ya zama mai tsada da rashin kuɗi don haɗa waɗannan ƙauyuka masu nisa zuwa tashar wutar lantarki ta ƙasa.

Wannan rashin wutar lantarki ya kawo cikas ga ci gaban al’umma da tattalin arziki da dama saboda rashin isassun wutar lantarki da ake buƙata ga gidaje da makarantu da ofisoshin ‘yan sanda da ɗakunan shan magani da kuma kasuwanci na cikin gida.

Wannan takarda tana ba da shawarar tsarin samar da wutar lantarki mai sabantuwa ga ɗaya daga cikin ire-iren waɗannan garuruwa masu nisa wato Semonkong a gundumar Maseru, Lesotho.

Samfurin binciken, yana daidaitawa da haɓaka tsarin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da bayanin amfani na garin Semonkong da wadatattun bayanan albarkatu masu sabantuwa na hasken rana da saurin iska da yawan kwararar ruwa daga Kogin Maletsunyane na kusa.

Ana amfani da softwaya ta HOMER don samar da ingantacciyar tsari dangane da mafi ƙarancin farashin wutar lantarki (LCOE) da matsakaicin ɓangaren makamashi mai sabantuwa, dangane da sababbin hanyoyin sabuntawa da madadin hanyoyin makamashi na sel na hasken rana da injin ruwa na iska da ƙaramin injin ruwa da janaretan dizal da kuma ma’ajiyar batir.

Ana gudanar da nazarin a hankali kan hasken rana da saurin iska da kwararar rafi da farashin dizal da buƙatun makamashi don kimanta yiwuwar tsarin wutar lantarki mai sabantuwa gabaɗaya wanda ya dace don aiwatarwa a wannan yanki mai nisa.

Sakamakon kwaikwaiyo don keɓantaccen ingantaccen tsarin dam/iska/PV/dizal/tsarin batir ya cim ma LCOE na dalar Amurka 0.289/kW a wani ɓangaren makamashi mai sabantuwa na 0.98.

Don haka, a ko da yaushe za a buƙaci janeratan dizal don ƙara ƙarfin wutar lantarki don Semonkong musamman a lokacin bushewa da sanyi na watannin Mayu zuwa Satumba lokacin da buƙatun makamashi ya kai ƙololuwarsa, amma hasken rana da kwararar ruwa sun kasance mafi ƙaranci.

Summary Title

Samar da makamashi mai sabantuwa abu ne mai yiwuwa ga Semonkong, Lesotho

Masu bincike sun ce yankin Semonkong mai nisa na Lesotho na iya rage farashin samar da wutar lantarki da kashi 40% ta hanyar haɓaka makamashi mai sabantuwa a cikin mahaɗar wuta ta gida daga kashi 66% zuwa 98%, ta amfani da iska da wutar lantarki da baturi da kuma wutar sel na hasken rana.

Janaretocin dizal kuma za su samar da sauran kashi 2%.

Ƙaramin garin Semonkong da ke gundumar Maseru, yana ɗaya daga cikin manyan duwatsu da kuma tsaunuka a Lesotho, wanda yake sa samar da wutar lantarki tsada.

Don haka, Semonkong a halin yanzu yana amfani da wutar lantarki da Kogin Maletsunyane na gida ke samarwa don samar da kashi 66% na wutar lantarki.

Sauran kashi 34% suna fitowa ne daga janaretocin dizal.

Manufar wannan binciken ita ce yin amfani da softwaya na HOMER (Hybrid Optimization Model for Electric Renewable) don ƙididdige iyakar ƙarfin wuta da za a iya samarwa ta amfani da albarkatun makamashi mai sabantuwa da ake samu a yankin a mafi ƙanƙancin farashi.

Masu binciken sun yi amfani da softwaya na HOMER don kwaikwayar mahaɗar wutar lantarki na gida na Semonkong a cikin kwamfuta ta hanyar gwada tasirin ƙara nau'o’in fasahohin makamashi da ake sabunta su kamar sel na hasken rana (makamashi daga hasken rana) da iska da wutar lantarki da ma’ajiyar batir.

Masu binciken sun lissafta Levelized Cost of Energy (LCOE) ga kowace mahaɗar wutar lantarki don gano nawa za a kashe tsawon rayuwar kayan more rayuwar.

Masu binciken sun gano cewa zaɓin mahaɗar lantarki mafi araha don Semonkong shi ne haɗin makamashi mai sabantuwa na hɗin iska da wutar lantarki da kuma baturi.

Wannan haɗin mahaɗar lantarki zai zama kashi 94% na makamashi mai sabantuwa, tare da kashi 6% na ƙarshe da janaretocin dizal za su samar.

Zaɓin tare da mafi girman rabon makamashi mai sabantuwa a kashi 98% yana ƙara sel na hasken rana zuwa gaurayawar mahaɗar lantarki mafi araha a sama, yana barin 2% kawai don samarwar jenaretocin dizal.

Idan aka aiwatar da waɗannan na'urorin kwamfuyuta na softwaya na HOMER, zai inganta haɗin wutar lantarki na yanzu na wutar lantarki mai sabantuwa daga Kogin Maletsunyane, wanda ya ƙunshi kashi 66%, tare da samar da kashi 34% da jenaretocin dizal za su samar.

Binciken ya nuna cewa haɗin tare makamashi mai sabuntawa kashi 98% zai rage farashin da kashi 40%.

Nazarin ya yi amfani ne da bayanai keɓaɓɓu ga Semonkong, wanda yasa sakamakon ya shafi Semonkong kawai.

Sai dai kuma wannan binciken ya nuna cewa ana iya amfani da albarkatun ƙasa kamar iska da koguna da wuraren da hasken rana ke da yawa wajen ƙara ƙarfin mahaɗar wutar lantarki ta gida da ta ƙasa a farashi mai rahusa.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?